Kannywood

Inuwa zafi : Adam a zango ya bayyana irin mawuyacin halin da yake ciki

Advertisment

Shahararren jarumi kuma mawaki adam a zango ya fadi irin yadda ya shiga yanayin rayuwarsa da ya shiga.

Adam a zango ya bayyana kuncin rayuwa wanda sam bai ji dadin halin rayuwa da yake ciki inda yayi fustin a shafinsa na sada zumunta a Instagram inda yake cewa:

“Wai shin idan na daina fim na daina waka na hakura da komai na nishadi za a barni in zauna lafiya?”

Ina cikin mawuyacin hali, kuma ba zan iya ci gaba da jurewa ba. “Ni burina kawai a yanzu in samu farin ciki ko da kuwa na mako daya ne, amma ba zan ci gaba da boye abin da yake raina ba.”

Hausaloaded ta tattaro martanin mutane akan Wannan maganar da adam a zango yayi.

@Baballehayatu cewa yake :

“Haba Adamu, me ya yi zafi haka?. Ina ga ai kamar mun yi wannan maganar, idan har akwai wani abu sai ka kira a waya kawai mu nemi mafita tare.

komai yai zafi maganin sa Allah..ba abunda yafi karfin Allah…haba adamu..Ina imanin ka ?ina tunanin ka?ina maganganun da muka zauna mukai mu da kai da ‘yan uwa da yawan mu..so,ya kamata mu sake zama.

@Ayshatulhumairah tana cewa :

Komai Yayi Zafi Maganin Sa ALLAH
Dukkan Abunda Yafi Karfin ka Bazai Fi Karfin Ubangijin Ka Ba
ALLAH Ta’ala Ya Kawo Maka Mafita A Cikin Rayuwar Ka Ya Yaye Maka Dukkan Damuwar Ka.

@safzorofficial cewa yake yi :

Allah ya Mana maikyau Allah Shine Masanin Komai Amma dauakka da Dadi Da wuya Haka kace a wata wakar ka Dan Haka ina mai Kara Baka Hakuri da Abarwa Allah Lamarin Zai yaye komai Dan Mazon Allah SAW. SIMBA ALWAYS SIMBA.

@sadisidi_sharifai yana mai cewa :

Ka mance da zancen nan babu wanda ya isa ya Hanaka sai ikon Allah.

@Ummabamalli ita cewa :

Babban Haidar kada ka bari kuncin rayuwa yayi tasiri akan ka dan girman Allah kayi hakuri ka kwantar da hankalin ka kodan yaran ka..ka sauka a social media nadan wani lokacin kome ze faru kace kada wanda ya fada maka inba abin farın ciki ze fada maka ba..katafi inda kasan hankalin ka ze kwanta sannan ka sami doctor wanda ze dinga duba lfy ka insha Allahu komai ze wuce kayi hakuri kowa da irin tashi lakar jarabawar ubangiji Allah ya fitar dakai Allah ka kawo maka dauki da gaggawa Allah ya baka mata daidai dakai wadda zata fahimce ka albarkaci ANNABI MUHAMMAD SAW muna rokon Allah ya duba lamarin ka Baba Haidar.

@sultan_abdurrazaq_doraya shima ya magantu inda yake cewa :

Bawai Iya film da waka bane kawai, kome kakeyi a wannan al’umma tamu, matukar kasamu daukaka acikinsa, kuma kace bazaka toshe kunnenka kuma ka kawar da kankaba, tofa mutane bazasu taba barinka kazauna lafiyaba. Sir ni ma baka shawara, da kayayyafawa zuciyarka ruwan sanyi, ta hanyar yi mata Abubuwan da takeso suke sakata nishadi. Kamanta da surutun mutane. Wlh Saudiya katafi kazama prop. Akan addini ka dawo kana kayar dashi. Matukar kasamu daukaka akan hakan toka gama zama lfy. Baga madaukaka a malaman nanba anbarsu sun zauna lfy. Ga misalai nan rututu. Dr. Ahmad. Yazauna lfy. Ina Albani zariya, ina sheik ja’afar. Ko Dahiru bauchi ba’a barshi yazauna lfy ba. Kana kan social media zaka sa’an jikansa yana Kiran sunansa ya zaginsa da sunan addini. Itafa a haka take. free advice

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button