Labarai

Leceister ta dakar da kocin na mata saboda zagin yana soyayya da ƴar wasarsa

Advertisment

Ƙungiyar ƙwallon ƙafar mata ta Leicester City ta fara bincike kan manajan tawagar Willie Kirk, game da zargin yana soyayya da wata daga cikin ‘yan wasansa.

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Leicester ta kuma dakatar da manajan sakamakon zargin, yayin da take gudanar da bincike kan batun. Don haka ba zai jagoranci tawagar a wasansu na Asabar ɗin nan ba.

Ƙungiyar ta fitar da sanarwa mai cewa “Willie Kirk yana taimaka wa kulob ɗin wajen gudanar da binciken na cikin gida, inda za a fito da sakamakon bincike a gaba”.

Sanarwar ta ƙara da cewa a yanzu mataimakiyar manajan ƙungiyar, Jennifer Foster da kuma mai horar da tawagar Stephen Kirby, za su ɗauki ragamar ƙungiyar a wasansu na yau da za su kara da ƙungiyar Liverpool ta mata.

Advertisment

Shi dai kocin da aka dakatar, Willie Kirk ya karɓi ragamar Leicester ne tun watan Yuli na 2022, lokacin da aka naɗa shi daraktan wasanni na ƙungiyar.

Daga bisani ya zama manajan ƙungiyar ranar 3 ga watan Nuwamba, inda ya maye gurbin Lydia Bedford.

A baya ma, Kirk ya taɓa jagorantar ƙungiyar Hibernian Women ta mata, da Preston ta maza, da kuma Bristol City, da ma Everton, kafin ya koma Leicester.

Haka nan kuma, ya taɓa zama mataimakin kocin Manchester United na ɗan lokaci a shekarar 2018.

A yanzu dai Leicester tana mataki na bakwai a teburin Women Super League ta Ingila, da maki 16 bayan wasanni 15. Kuma a yau za ta fuskanci Liverpool da ke mataki na biyar a gasar.

-TRT AFRIKA

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button