Labarai

Amurka ta karrama Limamin da ya ceci Kiristoci a Jos

Gwamnatin Amurka ta karrama wani Limami da ya ceci Kiristoci 262 daga wasu mahara inda ya boye su a masallacin da ke jikin gidansa.
Abubakar Abdullahi mai shekara 83, ya karbi lambar yabo ta ‘Yancin Addini ta duniya tare da wasu mutum hudun daga kasashen Cyprus da Sudan da Brazil da Iraki.
Tsallake Facebook wallafa daga U.S. Department of State

Karshen Facebook wallafa daga U.S. Department of State
Limamin ya ceci Kiristocin ne a garin Barkin Ladi na Jihar Filato a yankin tsakiyar Najeriya wadanda ke neman wajen tsira daga maharan.
Fiye da mutum 80 aka kashe a harin da ake zargin Kiristoci aka kai wa a yankin, kuma ba don agajin da limamin ya bayar na boye su ba da yawan wadanda suka mutun ya fi haka.
Limamin ya shaida wa BBC cewa ya yi taimakon ne saboda fiye da shekara 40 da suka gabata Kiristoci a yankin suka kyale Musulmai suka gina masallaci.
A wajen taron karramawar wanda Sakataren Harkokin Wajen Amurka Michael Pompeo ya gabatar, an bayyana cewa Liman Abdullahi ya sanya tasa rayuwar a hadari don ceto mabiya wani addinin daban da ke zama a yankin, wadanda ba don shi ba da an kashe su.

A kwanakin baya ne Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya gana da limamin aka kuma karrama shi da lambar yabo ta kasa.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button