Labarai

Kungiyar Atikun Jimeta Support Group Tayi Ikirarin Maka Atiku kotu in har Ya janye takararsa

Kungiyar Atikun Jimeta Support Group Tayi Ikirarin Maka Atiku kotu in har Ya janye takararsa

Kungiyar Atikun jimeta Support group, tayi tsokaci akan tana Rokon mai girma kuna dan takarar shugaban kasa, a karkashin tutar jam’iyar PDP wato Alhaji Atiku abubakar, kuma a madadin talakawan Nigeria wadanda suke ganin basuda wata hanya da zasu iya kawo kukan su Sai ta wannan reshe mai tuntubar ra’ayoyin talakawan Nigeria kuma kungiya mai kokarin ganin An samu sauyi da kuma shugaba adali a kasar mu nigeria,

Kamar yadda shi mai girma alhaji atiku Abubakar yayi bayanin cewa talakawa ne suka nemi daya fito Takarar shugabansa, saboda haka basu yarda ya hakura ya janye takararsa ba ya barwa wani bangaren ba, dan sunyi imanin cewa shi zai kawo sauyi na cigaba wa kasa sannan shi kadai suke da yakinin zai Gina rayuwar talaka, domin kuwa talakawan Nigeria sun tabbatar da nagartarsa da kuma adalcin sa, saboda haka in har ya janye takararsa to zamuyi karansa a kotu.

shugaban kungiyar Atikun Jimeta Support Group

Hon. Mu’awiyah Umar

08109934185.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button