Labarai
DA ƊUMI ƊUMIN SA | Jami’an Tsaro Sun Cafke Omoyele Sowore


Advertisment
Jami’an tsaro a Abuja sun cafke gawurtaccen dan tada zaune tsayen nan Omoyele Sowore mai gidan jaridar Sahara Reporters wadda ta kware wajen cin zarafin al’ummar Arewa a birnin tarayya Abuja.
Hakazalika, kamar yanda Sahara suka wallafa, an ji masa ciwo kafin a yi nasarar cafke shi tareda sauran abokanansa.
Idan dai baku manta ba, Omoyele Sowore yana daya daga cikin matasa da suka shirya zanga-zangar ENDSARS, wadda ta janyo asarar rayukka da dimbin dukiya a Arewacin Najeriya da kuma Kudanci.
Hakazalika, Omoyele Sowore ya sha yin ikirarin yi wa buhari zanga-zanga domin ganin an ham6aradda gwamnatinsa kamar yanda ya sha rubutawa a shafukansa na sada zumunta.

![[Bidiyo] Maroƙa sun rerawa Prof. pantami wakar Gwamnan jihar Gombe ta jawo cece kuce](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-11_18-55-03-999-scaled.jpg?resize=390%2C220&ssl=1)

