Labarai

Kotu tayi umarnin a rataye ɗan ƙasar China saurayin ummita

Advertisment

Babbar kotun jaha mai lamba 16 karkashin jagorancin mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji, ta zartas da hukuncin kisa ta hanyar rataya akan mutumin nan ɗan ƙasar China Frank Genk Quarong, wanda gumnatin kano ta gurfanar a gaban kotun bisa tuhumar kisan kai.

An dai samu Genk da laifi sakamakon shaidun da masu kara suka gabatar waɗanda suka tabbatarwa da kotun cewar, wanda ake tuhumar ya aikata laifin kisan kai akan wata matashiya mai suna Ummita wadda shaidun suka bayyanawa kotun cewar Frank Genk ya hallaka ta tun a ranar 16 ga watan Satumba na shekarar 2022 da misalin karfe 9 na dare.

Dalafm na ruwaito,Kotun ta gamsu da shaidun masu gabatar da kara guda 6, yayin da tayi watsi da shaidar kariya bisa rashin hujjoji, inda ta yi umarnin a rataye Genk har sai rai yayi halinsa.

Gabannin zartas da hukuncin lauyan dan china barrister Muhammad Dan,azumi ya roki kotun da ta yiwa dan chinan afuwa a karkashin sashi na 113 na ACJL sai dai kotun ta bayyana cewar wannan hurumin gwamnati ne.

Jawaban kariya da Frank ya yi a kotun sun yi nuni da cewar akwai soyayya tsakanin shi da marigayiya ummita, kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito mana labarin.

– Dala FM

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button