Labarai

Yan bindiga sun sace ƙawayen amarya fiye da mata 53 a jihar Katsina

Akalla mata yan kai amarya 53 ne yan bindiga suka sace a kan hanyarsu ta kai amarya a karamar Hukumar Sabuwa jihar Katsina

Lamarin ya afku a yankin garin Damari, kamar yadda wani da lamarin ya rutsa da iyalinsa ya sheka wa ta BBC Hausa.

A cewarsa, matan sun hau mota kanta kusan su 80, zuwa kai amarya bayan sun hadu da yan bindigar wasu sun sami damar tserewa, yayin da yan bindigar suka bugo masu waya cewa mutum 53 na hannunsu

Sai dai har kawo hada labarin hukumomin tsaro a jihar ba su ce komai ba game da shirin, kamar yadda majiyar ta BBC ta rawaito.

Karamar Hukumar Sabuwa na daya daga cikin kananan humumomi a jihar Katsina dake fama da matsalar tsaro tare da barazanar yan bindiga

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button