Kannywood

Shin da gaske Mawakiya maryam bakasee ta rasu?

Advertisment

A yau din nan anka wallafa a shafinta na Instagram @maryambakasee cewa ta rasu wanda nan take mutane suke wallafa suna yaɗawa cewa ta rasu.

Tabbas mutuwa rigar kowa ce amma bai dace mutane suna wallafa mutuwar mutum ba wanda bai mutu ba, ga abinda anka wallafa.

“Me account din nan tarasu”.

Shin da gaske Mawakiya maryam bakasee ta rasu?
Shin da gaske Mawakiya maryam bakasee ta rasu? Hoto/Instagram: maryambakasee

Wannan na sanya abokanan sana’ar ta nan take sunka karya ta a karkashin martani na fustin din suna cewa.

@ahmadshanawa : Me account din nan tarasu.

Wannan shi ya baiwa hausaloaded ta dukufa wajen binciken gaskiyar labarin inda take a shafinta na Tiktok @maryambakasee tana mai cewa.

Bayan sallama irin ta addinin musulunci ina yiwa kowa fatan alkhairi , yanzu anyi fustin a akawun dina na Instagram , akan na mutu , anzo anyi a tiktok , mutane suna ta kirana to wannan ba gaskiya bane.

Karya ake muku to ,ina ga ayi kutse a akawun din saboda kwana biyu banda lafiya , to shiyasa bansan wayayi ba, banda lafiya amma yanzu jikin alhamdullahi dan na samu sauki dan na samu sauki har an sallamu mu daga asibiti .

Mutanen da aka dagawa hankali ba laifi na bane kuyi hakuri- inji maryam bakasee.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button