Labarai
Yadda ‘Yan Fashi Suka Arce Da ‘Yan sanda Uku A Zamfara
Rahotanni daga jihar Zamfara sun nuna cewa wasu ‘yan bindiga dadi sun kai hare hare a kauyen Keta da ke cikin karamar hukumar Tsafe na jihar inda suka arce da wasu jami’an ‘yan sanda har guda uku.
Idan ba a manta ba, a watan Disamba na shekarar da ta gabata ne,gwamnatin jihar ta cimma wata yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan fashi da suka addabi yankunan jihar amma kuma a ‘yan kwanakin nan, an rika samun Rahotanni hare hare a wasu kananan hukumomi.
Sources:Rariya