Labarai

‘Yan bindiga na farautar rayuwata don ganin sun hallaka ni – Gwamna Dikko Radda

Gwamnan Katsina jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa, ya bayyana cewar ‘yan ta’addan da suka hana al’umma sakewa a jihar na farautar sa, amma kuma hakan ba zai sa ya daga kafa a kokarin sa na kakkabe su daga jihar domin tabbatar da zaman lafiya ba.

Gwamnan yace rahotannin tsaron da yake samu na tabbatar da haka, amma ko da sunan wasa babu abinda zai razana shi wajen ganin ya kauda kai daga alkawarin da ya yiwa jama’ar jihar sa na samar musu zaman lafiya.

Rada ya bayyana cewar nasarar da ake samu a kan ‘yan ta’addan shi ne ke musu zafi, saboda haka jami’an tsaro za su ci gaba da aikin su wajen ganin an samu cikakken zaman lafiya a jihar.

Yayin taron wanda ya samu halartar manyan sarakunan jihar, wato Dr Abdulmumini Jibrin, Sarkin Katsina da Dr Umar Faruk, Sarkin Daura da kuma shugabannin hukumomin tsaro, gwamnan yace duk da yake ba’a samu irin wannan zanga zangar a Katsina ba, yana da kyau a dauki mataki ganin yadda aka gudanar da ita a wasu jihohi cikin su harda jihar Kano dake makotaka da KatsinaKatsina, kamar yadda RFI Hausa ta rawaito mana

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin dake fama da matsalar tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya, amma kafa rundunar ‘yan sakai ya fara haifar da ‘da mai ido wajen kakkabe ‘yan bindigar da suka hana zaman lafiya a wasu kananan hukumomin jihar.

 

Wani labari : Gwamna Radda ya bada umarnin a rufe asusun ma’aikatun Gwamnati a jihar Katsina

 

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa, ya umurci kowace ma’aikata ta rufe asusun ajiyarta na banki don aiwatar da tsarin asusun bai-daya na TSA a harkokin shige da ficen kudaden jihar Katsina.

Radda “ya ce gwamnatinsa za ta aiwatar da tsarin TSA ne, domin karfafa tsarin kashe kudade a jihar. Wanda hakan zai taimaka wajen ganin an kashe kudaden gwamnati ta hanyoyin da suka kamata domin amfanin al’umma.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button