Abin da ya ja hankalina na rera wakar ‘Halitta’ – Nazifi Asnanic
Jaridar TRTAFRIKA Hausa ta samu tattaunawa da fitaccen mawakin nan naizifi Asnanic inda sunkayi masa tambayoyi da dama akan wasu abubuwa akan rayuwarsa da ma irin wakokin da sunke rerawa.
Nazifi Asnanic ya bayyana irin abun da ya ja hankalinsa wajen rera wakar “Halitta” wakar kuma ta samu karbuwa sosai duba da yadda mawaka yan uwansa sunka hau gasar wakar a manhajar tiktok wato “halitta challenge”.
“Shi duk wani marubuci ana so ya zamo mai kirkira to gaskiya na zauna ne na yi tunani mene ne zan yi wanda zai dau hankali kuma tittle din ga shi dai a fili amma hankali bai je kansa ba.Idan anka ce ‘halitta’ kaga abu ne wanda kamar za ka iya yi wa abubuwa da yawa wadanda suke magana a kan Wannan hallitar .
To ko da na dau tittle din shi kansa na farko ya dauki hankali don wadansu da sun kasa gane me ya sa zan ce halitta , daga baya kuma sai suka ga ai abu ne wanda kawai idan aka ce ga shi, to kawai misali in zana abu, ko na dauko abu na ajiye , sai na yi ta yabonsa, to haka na dinga yabon halitta din.
Nazifi Asnanic ya ƙara da cewa irin duk abin da aka yi wanda ya burge zaka iya yabonsa. To tun daga ‘title’ dai Allah da ikonsa title din ya dau hankali.- inji Nazifi Asnanic.