Labarai

Kotun taraiya da ta masana’antu ba su da hurumi akan rikicin masarautar Kano — femi Falana

Shahararren lauyan kare hakkin ɗan’adam ɗin nan mai muƙamin SAN, Femi Falana ya bayyana cewa babbar kotun tarayya da kotun masana’antu ta kasa ba su da hurumin yanke hukunci kan al’amuran sarauta.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a jiya Talata, Falana ya soki kotunan biyu kan yadda suka baiwa kansu hurumin sauraren ƙara a kan rikicin, inda ya ce hakan “kuskure ne matuka” da rashin gaskiya a karkashin sashe na 251 da 254 (C) na kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Ya ƙara da cewa wadannan hukunce-hukuncen sun saɓa wa hukuncin kotun koli da na kotun daukaka kara a kan lamarin.

Falana ya yi nuni da cewa yadda babbar kotun tarayya ta shiga cikin rigingimun da suka shafi tsige sarki Aminu Ado Bayero da kuma dawo da sarki Muhammadu Sanusi ll a matsayin rashin mutunta hukuncin da kotun koli ta yanke kan shari’ar Tukur da gwamnatin jihar Gongola (1987) 4. (117) 517.

A wannan shari’ar, Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa ƴancin zama sarki ba wani hakki ne na asali da tsarin mulki ya ba da shi ba, don haka babbar kotun tarayya ba ta da hurumin yin hakan.

Ya bayyana cewa, “Shiga babbar kotun tarayya a kan takaddamar da ta taso daga tsige Sarki Ado Bayero da sauran sarakuna da kuma batun dawo da Sarki Sanusi Lamido Sanusi ya saɓa da hukuncin Kotun Koli a Tukur da Gwamnatin Jihar Gongola ne,”

Daily Nigerian Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button