Ko kun san muhimmancin yawan yin jima’i ga lafiyar ɗan adam?


Ana bayyana sinadarin Oxytocin, da “sinadarin jiki na karin danƙon soyayya”
Shi ne sinadarin jiki da muke fitarwa idan muna tare da mutane da muka aminta da su, ko muke so.
Yana ɗaya daga cikin amfanin da sinadarin jiki na Hormones da ke samuwa a tsakanin iyali a lokacin jima’i.
Akwai hujjoji da aka sanar kawo yanzu da ke nuni da amfani na zahiri da na tunani a lokacin jima’i.
Kowane mutum na da irin nasa buƙata da tsarinsa. Za mu bayar da amfanin da dan adam zai iya samu lokacin jima’i, idan ana yawan yi a kai a kai.
Magance matsalar rashin barci
A lokacin saduwa, ƙwaƙwalwa na samar da wani sinadrin na endorphins, wato wani sinadari da ke samuwa a lokacin farin ciki ko jin daɗi, ko biyan buƙata.
Hakan dai na da alaka da shiɗewa da ake samu, kafin ko bayan inzali da hutu da samun nutsuwa bayan inzali
Duk da cewar yana sa mu jin dadi, ba za iya cewar jima’i na zama maganin damuwa ba.
Eh! zai iya samar da nishaɗi, da ke ƙara jin daɗi a tsakaninmu, amma cututtukan da suka shafi ƙwaƙwalwa na bukatar zurfafen kulawar likitoci.
Amma za mu iya cewa jima’i na sanya mutum bacci cikin sauƙi. Sai dai hakan na da kyau ga waɗanda ke fama da lalurar rashin bacci, da ake masa kallo da alamu na matsalar rashin lafiyar da ta shafi ƙwaƙwalwa.
Rage gajiya
Gajiya wadda tasirinta ya bambanta daga wani zuwa wani, wadda tana iya ƙaruwa ko ta ragu, inda hakan ke da alaka da buƙatu ko yayin ayyukan da mutum yake yi a rana. Hakan kuma na shafar sha’awarmu ta yin jima’i.
Idan muka jima a cikin shauƙi, shaawarmu na bukatar jima’i na raguwa, wanda hakan na haifar da rashin gamsuwa.
Yanayin barin sinadarin jiki na coristol ya hau na tsawon lokaci, da ke da matukar mahimmanci gare mu, wanda zai haifar da koma baya wajen jure buƙatunmu na yau da kullum.
A nan, hakan na nufin cewar, duk da jima’i na rage damuwa, jima’i na taimaka mana rage gajiyar da hakan ya haifar.
Wani abun sha’awa kan wannan batu shi ne, ma’aurata na jin daɗin saduwa da juna, idan suka gaji tikis.
Su ne kuma suka fi kowa amfana da tasirin jima’in.
BBC Hausa
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





