Boko haram: Abubuwan da sunka faru a zaman kotu tsakanin iyalan malam Ja’afar Mahmud da malam Nura Arzai
- Kotu ta bada belin Malam Nura Arzai, sannan an ɗage shari’ar zuwa 2 ga watan Nuwamba mai kamawa.
- Yayin zaman Kotun Majistiri mai lamba 23 da ke Noman Sland a Kano an tuhume shi da ɓata suna da yunƙurin tada tarzoma.
- Sai dai ya musanta zarge-zargen.
Gidan rediyon Freedom Radio kano sun samu zantawa da lauyoyin ko wane bangare akan yadda zaman kotun ta kaya.
“Sunana Barrister Ibrahim umar lauyan bangaren iyalan margayi sheikh Ja’afar Mahmud Adam kano abu ne sanane a nan kano shi wanda ake tuhuma malam nura arzai kenan ya fito a cikin wani bidiyo yana fadin marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam shine ya kirkiri boko haram kuma shine malamin su kuma yayi alwashin za’a yi yaki a najeriya .
Wanda yace su jami’an tsaro da sarakuna duk sun san da wannan to shine iyalan malam Ja’afar Mahmud Adam da suke da hakki da za’a cutar da babban su, shine yasa sunka kawo kotu a bi musu hakkinsu na wannan ɓata suna da ankayi masa – inji lauya Ibrahim Umar.
Shin yanzu anzo an karanta masa zarge zargen da ake masa ya musunta kuma gashi an bayar da belinsa hakan bazai kawo muku cikas ba?
“A’a ae babu komai tunda an bayar da sharudda wanda ankace idan an tayar da hankali za’a karya belinsa, saboda haka bamuda matsala tunda muna da hujjojin abinda yayi kuma zamu gabatar mu tabbatar a gaban kotu.
A karshe abinda muke so ayiwa iyalansa adalci da shi din ayi masa adalci akan abinda ake tuhumarsa kwata kwata ba haka bane.- inji lauyan bangaren iyalan margayi sheikh Ja’afar Mahmud Adam.”
Yanzu kuma zaku ji lauyan da yake kare wanda ake kara wato a bangaren malam nura Arzai kenan.
” Sunana Barrister Amjad nine wanda yake kare wanda ake kara malam nura arzai abinda ake tuhumarsa ya musunta kuma yana da hujjoji akan ya kare kansa saboda mu musan abinda yayi bai ɓata masa suna ba duk abinda ya fada yana da hujja da zai iya kare kansa”- inji lauyan malam nura arzai.
Ga bidiyon nan domin jin cikakken bayyanin.