Labarai

Yin jima’i akai akai na Rage hawan jini da ciwo

Yin jima’i a kai-akai na taimakawa wajen daidaita bugun zuciya da lafiyar zuciyar.

Bincike ya nuna yawan jima’i akai-akai tsakanin ma’aurata na rage hadarin kamuwa da hawan jini, musamman a daidai lokacin da ma’auratan ke matakin gamsuwa da kuma bayan hakan.

Idan matasa ko wadanda ke kan ganiyar kuruciya, suna yin jima’i akan kari misali kamar sau shida lokaci zuwa lokaci hakan na kara musu kuzari.

Wani bincike na baya-bayan nan, ya nuna cewar saduwa a tsakanin masu shekaru na rage musu matsalar bugun zuciya, amma sai dai yana da tasiri mai kyau, wajen rage wasu hadura da hakan ke tafe da shi. Yana kuma warkar da zafin bugun zuciya.

Inganta garkuwar jiki

Yin jima’i a kai-akai na ƙarfafa halittun da ke ba mu kariya a jikinmu daga cututuka.

Akwai bincike masu yawa da suke mawaharar cewar, saduwa sau uku a wata na taimakawa wajen kariya daga kamuwa da cutar korona.

Wannan bincike, shi ma na taimakawa wajen magance cuttkan da ake samu a lokacin jima’i.

Alfanun hakan ga sinadaran da ke yi wa jiki garkuwa, bai takaita da shekaru, ko a lokacin saduwa, kenan hakan na nufin kowa zai iya samun biyan bukata a lokaci daban-daban na rayuwarsa.

A taƙaice, hujjoji sun nuna cewar a lokacin da saduwa ke karuwa, garkuwar jikinmu na ƙara yaƙar dukkan wata barazanar rashin lafiya da ke mana barazana gare mu.

 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button