Yan sanda a katsina sun cafke matashi dan shan jini da ya kashe kawunsa


Rundunar ta yan sandan jihar Katsina tai nasarar cafke Nasiru Sanusi dan shekara 25 wanda ke gidan daudu a karamar hukumar Kankara
Kamar yadda mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Katsina Abubakar Saddiq ya gabatar da masu laifin a gaban manema labarai a yammacin yau Laraba 30 Oktoba 2024
A lokacin da yake wa manema labarai karin bayani kan ta’addacin da yai Nasiru Sanusi, yace ya hada kai da wasu gungun yan ta’adda inda sukayi garkuwa da kawunshi kamar yadda katsina post na ruwaito.
Sanan suka nemi abasu Naira miliyan 8 a matsayin kudin fansa da kuma buhun taki guda 6 inda bayan sun karbi abinda suka samu sai suka yanke shawarar kashe Kawun nashi
A lokacin da manema labarai ke tambayar Mai laifin Nasiru Sanusi kan cewa nawa aka bashi cikin kudin fansar da aka karba yace shi bai amshi komai ba
Bayan sun kashe Kawun nashi, sai ya tsallake zuwa jihar Legas inda can ne, ya hadu da yan kungiyar shan jini kamar yadda yake fadawa manema labarai cewa ya hadu da kungiyar yan shan jini
Ya cigaba da cewa idan yan kungiyar shan jini suna jin kanshi jini wani to sai aturashi yaje yayi yanda zaiyi har ya kawo abinda ake bukata ya cigaba da cewa ya kashe kamar mutum 10 a jihar Legas a tare da kungiyar Shan jini, daga bisani kuma yabar jihar Legas zuwa Taraba da Gombe inda can ma ya hadu gungu kala daban-daban na manyan yan ta’adda
Nasiru Sanusi a karshe ya shawarci iyaye da su daina sangantar da yaran su, wanda irin wanan ne ya sanya shi fadawa cikin wanan yanayin