Labarai

Magidanci na ta lalata da ‘ya ‘yanshi mata bayan rabuwa da mahaifiyar su

Wani magidanci dai yayi ta cigaba da yin lalata da ‘ya’yanshi ‘yan mata su biyu tun bayan rabuwa da yayi da mahaifiyar su wani lokaci can baya. Shafin Labarunhausa na ruwaito

Yara ne ‘yan mata su biyu

Kwamishiniyar walwala da jin ɗaɗin mata ta jihar Anambra tace an kama wani magidanci mai suna Nwobi, mai matsakaitan shekaru bisa tuhumar cewa yana lalata da ‘ya’yanshi mata su biyu; da mai shekara uku da kuma ‘yar shekara biyar.

Ma’aikatar walwala da jin ɗaɗin matan ce dai tare da haɗin gwuiwar jami’an tsaro na sibil difens suka yi nasarar cafke mutumin. Sun gudanar da samame ne kan mutumin a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoban nan da muke ciki.

Ance mutumin dai sun rabu da matar tashi tun wani lokaci a shekarar 2020, kamar yadda dai majiyar mu ta Punch ta ruwaito.

Magidanci na ta lalata da ‘ya ‘yanshi mata bayan rabuwa da mahaifiyar su

Likita ne ya tabbatar da anyi lalata da su

Kwamishiniyar walwala da jin ɗaɗin matan ta jihar Anambra Ify Obinabo, ta hannun mai taimaka mata kan harkokin watsa labarai Chidinma Ikeanyionwu, tace za’a hukunta wanda ake tuhuma nan bada jimawa ba.

Ta bayyana cewa bayan kuɓutar da yaran, an kaisu asibiti domin a duba lafiyar su, inda anan ne likitan dake kan aiki ya tabbatar musu da cewa lallai an taɓa yin lalata da ‘yan matan. Ta ƙara da cewa a lokacin da aka kaisu asibitin an samu raunuka a gaban su.

Da aka ji ta bakin yaran, sun tabbatar da cewa mahaifin nasu yana lalata da su, kuma su basu sha’awar ƙara komawa gidan nashi domin gudun abinda ka iya zuwa ya dawo.

Wanda ake tuhuma ya musanta

Sai dai kuma wanda ake tuhuma ya musanta zargin, inda yace baya da masaniya akan cewa wani yana yin lalata da ‘ya ‘yanshi ballantana kuma ace shi karan kanshi. Yasha alwashin ɗaukar mummunan mataki akan wanda ya zo ya kawo ƙarar shi kan hakan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button