Labarai

Saurayi da budurwa sun daurawa kansu aure asirance

Advertisment

Wasu matasa sun daurawa abokinsu aure da budurwarsa ba tare da sanin iyayensu ba. Wannan al’amari mai kama da al’amara ya faru ne a unugwar Gandun Sarki cikin karamar hukumar Mallam Madori a jihar Jigawa.

Majiyar Leadership hausa na ruwaito Matashin mai suna Yahaya Isa wanda aka fi sani da Badi, kamar da wasa yace idan budurwar ta amince su yi aure yanzu ma ga sadaki a hannunsa.

Saurayi da budurwa sun daurawa kansu aure asirance
Saurayi da budurwa sun daurawa kansu aure asirance

Nan take kuwa budurwar mai suna Sa’a ta ce, ta amince su yi aure. Anan ne abokai suka hadu aka daura auren har ma aka bayar da sadakin N15,000 da zimmar za a ciko N35,000 a matsayin kudin sadaki.

Sheik Yusuf Abdurrahman, Limamin masarautar Hadejia na daga cikin malaman addinin da suka bada fatawar cewa aure ya dauru.

Advertisment

Karanta Wani labari : Yaudara ko ganganci : budurwa ta shafe shekara 8 suna soyayya da saurayinta,amma yayi mata kan mage ya waye

Maryam Nuruddeen Shuwa Gwammaja ta bayyana yadda Saurayinta ya yi mata Yankan Kauna bayan shafe shekaru 8 suna Soyayya.

Ta ce ya rika bata kudi tana siyo kayan lefe ashe wata take hadawa sai saura kwana daya aurensa ta gano abin da ya dangana da ita zuwa gadon Asibiti.

Maryam nuradeen shuwa ta fara bada wannan labarin a kafar sadarwa ta titkok inda wannan labarin yayi matuƙar tayar da kura a kafaffen sada zumunta.

Gidan rediyon Dala fm kano sun samu zantawa da yarinyar inda ta basu labarin yadda soyayyar su ta fara har i zuwa lokacin kacin da yayi kan mage ya waye yayi wuff da wata ya barta da gadon asibiti.

Maryam yar shuwa tana cewa :

“Daga wasa soyayya ta fara amma daga baya ta lalace, na fara son shi ne ta dalilin wata yar uwarsa wanda takai kala bana kula shi har ina kula shi muna soyayya sosai mun shaku mun dauki tsawon shekara 8 muna soyayya.

“Muna muna soyayya sai maganar aure ta shiga gidan su an sami nema gidan mu an sani”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button