Labarai

Mota ta buge wani barawon waya a Kano – ‘Yan sanda

Advertisment

Bayan mota ta buge mutumin da ya zare danbida ya kwaci wayar wata mata, an gano cewa kashin bayansa ya karye kuma kansa ya fashe”, in ji kakakin ‘yan sandan Kano Abdullahi Haruna Kiyawa.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta ce mota ta buge wani mutum da ya yi kwacen waya yayin da ya sheka a guje domin tsallaka titi a cikin birnin na Kano.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi da maraice.kamar yadda majiyarmu ta TRTAFRIKA na ruwaito.

Mota ta buge wani barawon waya a Kano - 'Yan sanda
Mota ta buge wani barawon waya a Kano – ‘Yan sanda

“Yanzu na samu rahoto daga Zoo Road cewa wani ya zare danbida ya kwaci wayar wata mata. Yana tsallaka titi mota ta kade shi. Ana bukatar mu kai shi asibiti,” in ji Abdullahi Kiyawa.

Sai dai daga bisani kakakin ‘yan sandan na Kano ya sake wallafa wani sako da ya nuna cewa mutumin da ya kwaci wayar yana cikin mummunan yanayi.

Ya ce: “Bayan mun kai (mutumin da ya kwaci waya) asibiti yana dan motsi, kashin bayansa ya karye kuma kansa ya fashe”, inda ya kara da cewa asibitin suna tunanin kai shi sashen bayar da kulawar gaggawa.

Jihar ta Kano ta yi kaurin suna game da matsalar masu kwacen waya. Sau da dama sukan kashe mutum ne sannan su kwace wayarsa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sha kama masu kwacen waya tana gurfanar da su a gaban kuliya. Sannan tana fitar da bayanai a-kai-a-kai game da yadda mutane za su kauce wa wannan matsala.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button