Labarai

Yadda zaka Duba Idan kayi Nasarar Samun Aikin Yan sanda

Advertisment

Yadda zaka Duba Idan kayi Nasarar Samun Aikin Yan sandaSakamakon umarnin da Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya ya bayar wa shugaban ‘yan sandan Nigeria Maigirma IGP Alkali Usman Baba, rundinar ta shirya tsaf domin cigaba da daukan sabbin ‘yan sanda masu mukamin Constable dubu goma (10,000) wanda aka fara tun shekaran da ta gabata 2020
An fitar da wannan link ranar Litanin 18-10-2021 rundinar ‘yan sandan Nigeria zata bude shafinta na yanar gizo, wanda ya san ya nemi aikin ‘yan sanda a shekaran da ta gabata 2020 kuma ya halarci gurin physical and credentials screening ya shiga ya duba sunansa ko ya tsallake
Wadanda suka samu nasaran tsallake physical/credentials screening zasu samu damar rubuta jarabawa na karshe daga ranar 29 zuwa 30 a wannan wata na October da muke ciki, wannan shine shafin da za’a shiga a duba https://www.policerecruitment.gov.ng/#/status/nin/verification
Za’a bude shafin daga jibi Litinin 18 zuwa ranar 26 ga wannan watan.

Yadda zaka Duba Idan kayi Nasarar Samun Aikin Yan sanda
Yadda zai bude sai ka snya NIN/Reference Id/Lamba waya/ Email

Duk wanda ya shiga shafin ya ga ya samu nasaran tsallakewa to yayi printing examination slip dinsa wanda za’a yi amfani dashi a gurin rubuta jarrabawa da za’a fara ranar Juma’a 29 zuwa 30 ga wannan wata, rundinar ‘yan sanda tana shawartan jama’a da suka cika neman aikin su dinga duba sakonnin email da nambar wayoyinsu.
Rundinar ‘yan sandan Nigeria tana kara tabbatarwa al’ummar Nigeria cewa wannan tsarin nata na diban sabbin ‘yan sanda masu mukamin Constable kyauta ne, rundinar tace duk wani mai neman karin bayani zai iya tuntubarta akan wannan layin waya 08100004507
Yadda zaka Duba Idan kayi Nasarar Samun Aikin Yan sanda
Wannan shine idan ka samu nasara zakagani

Sanarwa daga Kakakin ‘yan sanda na kasa CP Frank Mba
Arewa Intelligence
16-10-2021
Muna fatan Allah Ya bawa mai rabo sa’a
Ga link nan kasa sai ku shiga.
https://www.policerecruitment.gov.ng/#/status/nin/verification
NB: Akwai wadanda sunka samu sakon congratulations.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button