Labarai

[Bidiyo] Allah kada ya bani haihuwa koda Nayi Aure cewar wata Budurwa ya jawo cece kuce

Advertisment

Wata mace wadda ta amsa sunan ta mace ta kowace fuska, ta fitar da wani bidiyon ta tana mai bayyana wani sharadi ga duk namijin da ya yadda zai aure ta.[Bidiyo] Allah kada ya bani haihuwa koda Nayi Aure cewar wata Budurwa ya jawo cece kuceA cewar ta tana so tayi aure, amma bata son yaya bata son ta haihu, ko da kuwa da daya ne.A cewar ta yaya wahala ce zalla samun su a rayuwa, saboda kula da su, dawainiyar su, basu tarbiyya, na daga cikin abinda ya sanya kwata kwata bata sha’awar su

.”Ina mamakin matan dake zumudin aure domin su Haihu, wata tace tana son yaya 3, wata 9, wata goma sha, mhn Ni tab ko daya bana sha’awa.”

”Wai to da suke son ya’yan sun manta da dawainiyar su, basu kulawa, gaskiya bana sha’awar samun su kwata kwata.”

”Dama sai na gayawa duk wanda zan aura cewa Ni fah bana sha’awar haihuwa, kuka ba zan haihu ba, saboda ban shirya wannan wahalar ba.”

Inji ta.Yanzu haka dai bidiyon ta na ci gaba da yawo a shafukan sada zumunta, musamman Facebook.

Kalli bidiyon a Nan

Mutane sun tofa albarkacin bakin

 su@namama.1 ya rubuta:“Ba kiyi laifin komai ba ƴar’uwa, na yi fatan cewa iyayen ki sun san hakan kafin su haife ki. Da basu haifa Jaka mummuna mace irin kiba.”

@for.hanadra ya rubuta:“Babu komai don kin bayyana ra’ayun ku, amma yakamata ace kin bar hakan a zuciyar ki tunda baki san inda ze ƙare ba ko yadda za a fassara ba.”

 

@hikmagil ya rubuta:“Mutane masu cewa Insha Allah ba zaki haifi ko ɗaya ba, kada ku manta yayin da kuke addua ga wani, kuma ana yi muku makamanciyar ta.”

 

@eyshaluv1 ta rubuta:“Subhanallah ina son yara Allah ka albarkaceni da yara. Don Allah ku sanya ni a addu’a ina son yara shekara ta 6 da aure yanzu.”

@khadijaluv ta rubuta:“Ina tunanin na fahimce ki, shekarun ki ne kawai suke magana, zan so jin haƙiƙanin yadda zaki ji shekara uku kacal bayan auren ki.”

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button