Labarai

Abin Mamaki Shugaban Kasa Da Gwamna Na Kallo Ana Kashe Al’umma A Jihar Zamfara, Cewar Sheikh Yusif Samb Rigachikun

Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano

Babban Malamin addinin islama dake Kaduna mataimakin Shugaban majalisar malamai ta kasa na kungiyar Izala ya yi  kira da babban murya akan abinda yake faruwa a jihar Zamfara tun daga Gwamnatin jiha har zuwa Gwamnatin tarayya. Akan cewa ya zama dole su dubi girman Allah du kuma dubi girman ran Dan Adam yadda Allah ya karrama ya kuma ba shi muhimmaci.

“Ya wajabta wa Dan Adam kiyaye lafiyar kansa da kansa. Balle rayukan da ya ta’allaka ga shugabanninmu wurin tsare ta da kiyayeta. Da kula da lafiyarta. Amma abun mamaki yau gashi jihar Zamfara ta zama jihar zubar da jinin al’umma. Gwamna yana gani Shugaban kasa yana gani.

“Mministan tsaro dan jihar Zamfara ne. Shi ma yana Gani. Amma ba a dubi wannan al’amari ba har yanzu”.

Sannan Sheikh ya yi karin bayani da cewa yaya shugabanni suke tunanin amsa tambayoyi a gaban Allah gobe kiyama akan jinin wadannan bayin Allah ranar da za’a tsaida ko wane rai da wanda Allah ya ba shi hakkin kiyaye kula da shi amma bai kiyaye kiwon da Allah ya ba shi ba?

“Kuma babban abun mamaki yau idan aka ce wani babban jami’in Gwamnati aka kashe to sai a dauki kwararan matakai wurin ganin sai an gano sanadiyar kashe shi kamar yadda ya faru a hanyar Kos. Da kuma kokarin gano makasan Alex Badeh.

“To amma ga milyoyin al’umma ana ta kashewa kace kamar dusa ake shukawa shiru kake ji”.

Sheik ya kawo Hadisi ingantacce akan abun da ya faru da Usama. Lokacin da wani ya yi sata cikin kabilarsa ganin cewa dan babban gida ne.sai ya zo ya nemi a yafe masa. Manzo Allah (SAW) ransa ya baci akan haka. Daga karshe Annabi ya ce mutanen sun kusan halaka har idan wani daga cikin manyan kasa zai yi laifi a bar shi. Idan kuma talaka yayi laifi sai a tsaida haddi akansa a kan kashe ran mumini guda daya. Kuma dole mu fita mu fadawa kawunan mu gaskiya don kuwa yanzu ga ‘yan agajinmu a hannun irin wadannan mutane. Ba mu san halin da suke ciki ba. Allah ya bamu zaman lafiya a kasarmu”.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button