Labarai

Kwaɗayi ko Rashin imani : An kama barayin janareton masallaci a Kaduna

Advertisment

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zarginsu da satar janareta da batirin da ke haska futilun masallaci mai amfani da hasken rana a wani masallaci da ke Kaduna.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Mansir Hassan, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a Kaduna ranar Asabar.

Dclhausa na ruwaito cewa Mansir ya ce jami’an tsaro sun kama fara kama daya daga cikinsu mai suna Basiru Rabiu da ake zargin a unguwar Sabon Gari da ke karamar hukumar Hunkuyi.

Sanarwar ta bayyana cewa yadda aka hangi mutumin na labewa tare da yin kwanto a kusa da Masallacin Juma’a suka nuna shakku kuma aka kama shi.

Yayin da ake yi masa tambayoyi, ya amsa laifin cewa ya saci janareta da batir mai amfani da hasken rana a masallatan kauyen Hunkuyi da Nahuce.

Inda ya tabbtar da cewa ya sayar da kayan da ya sata ga wani mutum msi suna Mansir Umar wanda shi ma yake a hannun jami’an tsaron.

Wani labari na daban : Ɓarayin Daji Sun Ƙona Motar Kayan Amare A Jihar Katsina

Yadda ɓarayin daji suka tare motar kayan Amare tsakanin ƙaramar hukumar Jibia zuwa ƙaramar hukumar Batsari jihar Katsina.

A daren ranar Talata 08/01/2024 ne ƴan ta’addar daji dake kan hanyar Jibia zuwa Batsari suka tare wata mota ɗauke da kayan wasu Amare guda Ukku da suka haɗa da Gadaje Kujeru da Katifu guda huɗu, Inda basuyi wata wata ba suka banka masu wuta. Wani mai amfani kafar sada zumunta ta Facebook Muhammad aminu kabir na ruwaito wannan labari.

Ɓarayin dai sun hana Direban da yaron shi fita daga Motar Inda suka ƙone ƙurmus tare da kayan da suke ɗauke dasu.

An samu gawar Direban mai suna Babangida Garba Turaki wanda akayi mashi sutura a jiya amma shi yaron Motar Auwal Malle ba a ma Iya samun gawar shi ba domin ya ƙone ya zama toka ko Gawayi.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button