Duk Mutumin Da Muka Kama Da Laifin Yin Fyade A Jihar Kaduna, Za Mu Rataye Shi Har Lahira ~ Gwamna El-rufa’i
Daga Comr Abba Sani Pantami
A daidai lokacin da jama’a su ke kira da babbar murya ga gwamnatoci da su kawo karshen matsalar fyaden mata da kananan yara, gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana inda ta sa gaba.
Mai girma gwamnan jihar Kaduna, ya bayyana cewa sai inda karfinsa ya kare wajen ganin doka ta yi aiki a kan duk wadanda aka kama su na aikata wannan barna a cikin jiharsa.
Kwamishinar harkokin mata ta Kaduna, Hafsat Mohammed Baba ta bayyana cewa gwamna Nasir El-Rufai zai rattaba hannu a kan dokar kashe masu laifin fyade a jihar Kaduna.
Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai ta ce da gaske ta ke yi wajen kawo karshen matsalar fyade da ake samu. Gwamnati ta kuma yi kira ga mabiya su bada goyon bayansu a yakin.
Hajiya Hafsat Mohammed Baba ta bayyana wannan matsaya na gwamnan Kaduna ne a shafinta na Twitter.
Jama’a sun fito su na tofa albarkacin bakinsu game da wannan lamari, inda wasu su ka nuna goyon bayansu ga gwamnatin, yayin da wasu kuma su ke ganin akwai gyara a matakin.

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




