Ƴan bindiga sun kashe Limami da wasu mutane 2, sun yi garkuwa da mutum 32 a jihar Katsina
Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a garin Ƴandaka, sun kashe mutum 3 ciki har da limanin garin mai suna Mal. Basiru Jibrin, inda suka yi garkuwa da a ƙalla mutum 32, zuwa daji don neman kuɗin fansa, a ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina.
A zantawar Katsina Reporters ta yi da wani mazaunin yankin ya shaida mana cewa ƴan bindigar sun shigo garin, a daren ranar Talata da misalin karfe 9:00pm na dare inda suka shiga gidaje suka ƙwashi tsakanin mata da maza da ƙananan yara.


Majiyar Katsina Reporters ta samu cewa, daga cikin mutanen da da ƴan bindigar suka yi garkuwa dasu aƙwai limanin garin Mal. Basiru Jibrin da Abdullahi Yusuf da wani ƙaramin yaro
ƴan bindigar sun ci karen su ba babbaka wanda suka shafe fiye da awa ɗaya suna bi gida-gida suna ƙwasar mutane tare da yin awon gaba da su zuwa daji, don neman kuɗin fansa.
Karamar hukumar Batsari dai na fuskantar sabbin hare-haren ‘yan bindiga a baya-bayan nan. Wanda cikin mako guda, ‘yan bindigar sun kai hari kusan huɗu a yankin.
Wani Labari : Yan bindiga sun sace mutum 35 a jihar Katsina
Wasu yan bindiga ɗauke da miyagun makamai sun kai hari a garin Tashar Nagulle, inda suka yi garkuwa da a ƙalla mutum 35 zuwa daji don neman kuɗin fansa, a ƙaramar hukumar Batsari, a jihar Katsina.
A zantawar da Katsina Reporters, ta yi da wani mazaunin yankin ya shaida mana cewa ƴan bindigar sun shigo garin Tashar Nagulle, a daren ranar Lahadi, da misalin karfe 9:30 na dare, inda suka yi ta harbe harbe saman iska wanda suka bi gida gida suka ƙwashi a ƙalla mutune 35 zuwa daji don neman kudin fansa.
A cewarsa, ba zato babu tsammani ƴan bindigar suka shigo garin suka ƙwashi mutanen tsakanin maza da mata da ƙananan yara, ba tare da samun ɗaukin jami’an tsaro ba, wanda lamarin yayi matuƙar ta-da masu hankali.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





