Labarai

Yan bindiga sun sace mutum 35 a jihar Katsina

Advertisment

Wasu yan bindiga ɗauke da miyagun makamai sun kai hari a garin Tashar Nagulle, inda suka yi garkuwa da a ƙalla mutum 35 zuwa daji don neman kuɗin fansa, a ƙaramar hukumar Batsari, a jihar Katsina.

A zantawar da Katsina Reporters, ta yi da wani mazaunin yankin ya shaida mana cewa ƴan bindigar sun shigo garin Tashar Nagulle, a daren ranar Lahadi, da misalin karfe 9:30 na dare, inda suka yi ta harbe harbe saman iska wanda suka bi gida gida suka ƙwashi a ƙalla mutune 35 zuwa daji don neman kudin fansa.

A cewarsa, ba zato babu tsammani ƴan bindigar suka shigo garin suka ƙwashi mutanen tsakanin maza da mata da ƙananan yara, ba tare da samun ɗaukin jami’an tsaro ba, wanda lamarin yayi matuƙar ta-da masu hankali.

Ƙaramar hukumar Batsari na ɗaya daga cikin garuruwan da suke fama da matsalar tsaro a Katsina wanda ake ka-she jama’a tare da yin garkuwa da mutane, don neman kudin fansa.

Wani labari: Farashin Gyaɗa da Riɗi sun yi tashin Gwauron zabi a kasuwannin jihar Katsina

A wannan makon farashin Gyaɗa da Riɗi a kasuwannin jihar Katsina ga yadda farashin yake a kasuwar Batsari da wasu kasuwanin.

1- Buhun Masara – 52,000
2- Buhun Dawa – 44,000 _ 46,000
3- Buhun Gero – 48,000 _ 50,000
4- Buhun Shinkafa –
5- Buhun Gyada – 76,000 _ 100,014 Mai bawo – 28,000
6- Buhun Wake – 76,000
7- Buhun Waken Suya – 48,000
8- Buhun Rogo – 46,000
9- Buhun Dankali – 17,000
10- Buhun Barkono – 48,000

Kasuwar garin Kankiya, ga yadda farashin sa yake Kamar haka;
1- Buhun Masara – 55,000
2- Buhun Gero – 45,000 _ 46,000
3- Buhun Dawa – 42,000
4- Buhun Shinkafa tsaba – 96,000
5- Buhun Gyada – 100,000 Mai bawo – 22,000
6- Buhun Wake – 68,000
7- Buhun Waken suya – 44,000
8- Buhun Alkama – 60,000
9- Buhun Ridi – 150,000
10- Buhun Aya manya – 44,000 kanana – 38,000
10- Buhun sobo – 20,000
11- Buhun Dankali -20,000

Kasuwar garin Dandume, ga yadda farashin sa yake kamar haka;

1- Buhun Masara fara – 49,000 ja – 48,000
2- Buhun Dawa – 44,000
3- Buhun Gero – 48,600 Dauron – 48,000
4- Buhun Alabo – 28,000
5- Buhun Wake ja – 65,000
6- Buhun Waken Suya – 43,000
7- Buhun Gyada tsaba Fara – 77,000 ja – 80,000 mai bawo – 25,000
8- Buhun Shinkafa tsaba – 95,000 shenshera – 38,000 ta tuwo – 98,000
9- Buhun Dabino – 140,000
10- Buhun Aya – 55,000 kanana – 50,000
11- Buhun Dankali – 16,000 makani – 28,000
12- Buhun Tarugu – 35,000 solo – 20,000
13- Kwandon Tumatur – 7,000 kauda – 45,000
14- Buhun Tattasai kauda – 50,000
15- Buhun Alkama – 60,000
16- Buhun Albasa – 60,000

Kasuwar garin Dutsinma, ga yadda farashin sa yake Kamar haka;

1- Buhun Masara – 50,000 _ 52,000
2- Buhun Dawa – 42,000 _ 44,000
3- Buhun Gero -50,000
4- Tiyar Ridi – 1,700
5- Tiyar Shinkafa – 2,200 _ 2,300
6- Tiyar Gyada Mai bawo – 650 _ 700
7- Buhun Wake – 60,000
8- Buhun waken suya – 46,000 _ 48,000
9- Buhun Tattasai – 10,000
19- Buhun Tarugu – 15,000
11- Kwandon Tumatur – 1,500

Rahoto daga:
Aisha Abubakar Ɗanmusa.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button