Masu magunguna a kasar Hausa ‘yan Damfara ne – Baba Impossible


Fitaccen masanin bokanci da tsubbace-tsubbacen nan Muhammad Tahar Baba Imposible, ya ce ‘yan damfara da masu magungunan bogi sune kaso mafi rinjaye a cikin masu bada magungunan da ake da su a kasar Hausa.
Muhammad Tahar Baba Imposible ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da gidan rediyon Dala FM, da safiyar Larabar nan.
“‘yan kadan ne daga cikin masu bada magungunan da ake da su na gaskiya, amma kaso masu yawa duk masu damfara da cutar al’umma ne tare da bada magungunan akan hanyar da ta saba da tsarin shari’ar musulunci, “in ji shi”.


Wakilinmu Ibrahim Abdullahi Soron Dinki ya rawaito cewa Baba Imposible ya kuma ce, za’a samu mafita ta hanyar wayar da kai mai-makon mayar da hankali wajen kafirta masu yi, sannan kuma a rage cutar da mata a gidajen aure wanda hakan ne yasa suka fi yawan mu’amula da masu damfarar sakamakon matsananciyar bukata da take korarsu.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




