Labarai

Burin Zuciya : Allah Ya bani Miji Dan Wanka Da iya kwaliya kamar Sanusi II – Inji Wata Tsalelliyar Budurwa

Advertisment

Sanusi lamido sanusi II wanka kamar dawaisu

Fitacciyar mai amfani da shafukan sadarwa na zamani musamman shafin Facebook, kuma malama a jami’ar jihar Kaduna (KASU), Bilkisu Sani Yero wacce aka fi sani da Arewa Queen, ta yi addu’a akan Allah ya bata mutumin da ya iya kwalliya tamkar tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II.
Balkisu Sani Yero (Arewa Queen)

Arewa Queen da ta ke koyarwa a sashen nazarin halayyar ɗan adam a jami’ar ta KASU, ta bayyana hakan ne a shafinta na facebook, da yammacin yau Talata, inda masu bibiyar ta a shafin su ka tofa albarkacin bakinsu akan lamarin.
Bisa al’adar ƙasar Hausa dai namiji ne yake ganin mace idan hankalinsa ya kwanta da ita sai ya tura iyaye ko manyansa a nema masa izinin har a kai matakin soma batun aure.
Sanusi lamido sanusi II

Amma sakamakon juyin zamani da ya zo da abubuwa masu yawa da sunan wayewa, domin mace kan iya ganin namiji ta furta hankalinta ya natsu da shi ko tana fatan ya aure ta.
Sanusi lamido sanusi Dan kwalisa

Haka kuma ba wannan ne karon farko da mace ke bayyana fatan samun namiji mai wata dabi’a ko siffata ta fitattun mutane ko kuma so bayyana kai tsaye shi fitaccen mutumin su ke so. Domin ko a ɗan kwanakin nan sai da aka samu wata budurwa tana furucin kafatanin mazan duniya babu wanda ta ke so kamar Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
me zaku iya cewa?

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button