Labarai

Makiya Zaman Lafiyar Nigeria Sun Fara Bayyana Kansu (Hotuna)

 
Daga shekaran jiya zuwa yau masu zanga-zangar ENDSARS sun aikata munanan ta’addanci, kama da ga kashe jami’an tsaro rusawa da kone ofisoshin ‘yan sanda da kayan gwamnati, fasa gidan yari, fasa gurin ajiyar kayan abinci na hukumar kwastom, kone dubban motoci da fasa shagunan mutane
Na ga bidiyon yadda suka fasa Banki First Bank a Lagos suka kwashe kudi, har injin ATM na bankin ba su bari ba sun tafi da shi, sannan suka bankawa bankin wuta, sannan na gansu rike da bindigogin jami’an tsaro wanda suka kwace a ofishin ‘Yan sanda, sun kashe ‘yan sanda sun kwabe kayansu sun sanya a jikinsu
Datti Assalafy ya kara da cewa duk wannan ta’addanci da masu zanga-zangar ENDSARS ke yi bai sa makiya zaman lafiyar Nigeria sun fito sun nesanta kansu da su ba, sai bayan da a daren jiya ‘yan sandan kwantar da tarzoma da sojoji suka fara dakilesu, sai gashi yanzu sun fito suna sukar rundinar tsaron Nigeria da gwamnatin shugaba Buhari
Dukkan hujja da dalilai da gwamnatin Nigeria zata dogara da shi wajen daukar mataki akan wadannan ‘yan ta’adda ta samu, ko a Kasar Amurka ne abinda zasu yi kenan wajen daukar mataki
Yaa Allah Ka kunyata makiya zaman lafiyar Nigeria Amin.
Ga hotunan kasa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button