Labarai

Zamu Sake Gargame ku Idan Cukoso Yaci Gaba – FG

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa za ta sake kulle wasu sassan kasar nan matukar cutar coronavirus ta ci gaba da yaduwa.

Shugaban hukumar kula da hana yad war cututtuka ta NCDC, Dr Chikwe Ihekweazu, ya ce duk da hukumar na zaton za a samu masu karya doka, amma hankalinta ya tashi da yadda ta ga ana turereniya a bankuna a yau Litinin.

A yayin jawabi ga manema labarai daga kwamitin yaki da cutar na fadar shugaban, shugaban NCDC din yace: “Rahotannin farko na fadin kasar nan basu da dadin ji. Idan muka ce a kiyaye, da gaske muna nufin a kiyaye.

“Babban wurin da muka amincewa da su bude kasuwancinsu a yau sune bankuna.

“Idan kuka kayyade yawan wadanda za ku bude, dole kowa ya nufa inda kuka bude daga nan a samu cunkoso.

“Za mu iya bada tarin dokoki amma idan baku kawo tsarikan da za ku taimaka ba, ba za su yuwu a bi su ba. Daga nan kokarinmu zai tashi a banza.”

Ya kara da cewa, “A yau za mu iya daga kafa kadan saboda ita ce rana ta farko. Amma akwai yuwuwar mu samu masu cutar da tarin yawa saboda babu wanda ya bi doka.

“Amma abu mafi muhimmanci shine yadda za mu kiyaye daga kuskurenmu a gobe. Hakan ne kadai zai sa komai ya koma daidai kafin ranar Juma’a.”

Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, ya kara da cewa: “Tabbas mun san za a samu matsala saboda an bude jama’a, amma babban kalubalen shine yadda zamu kiyaye nan gaba. Bamu son karuwar masu cutar.

“Idan muka samu hakan kuwa, bamu da zabin da ya wuce mu sake mayar da jama’a gida don kulle. Don haka kiyayewa ce mafita.”

A gefe daya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya da su tallafawa kasashe mambobinsu wajen rage radadin da annobar cutar korona ta jefa su a ciki.

Domin neman hadin gwiwa, Buhari ya bukaci Asusun Bayar da Lamuni na Duniya da kuma Bankin Duniya, da su taimakawa kasashe mambobinsu wajen dakile mummunan tasirin da annobar cutar korona ta yi sanadi.

Daga cikin taimakon da shugaba Buhari ya nema akwai bukatar tsawaita lokacin dawo da rancen kudade, tallafin fasaha, rage jadawalin kudin fito a kan kayayyakin kiwon lafiya da kayayyakin masarufi.

#legithausa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button