Labarai

Jahilci Ko Son Rai Ke Sa Wasu Cewa Bai Kamata Malamai Su Shiga Siyasa Ba – Prof Pantami

Advertisment

As sheikh farfesa Ali isah pantami ya zamu zantawa da gidan rediyon murya Amurika voahausa kenan kan yadda mutane suke kallon bai dace malamai su shiga harka siyasa ba.

Inda wasu ke ganin abarta kawai ga wadanda sunka kira kansu yan siyasa da kayansu shi kuma malami yaje wajen karantarwasa da wa’azi shine abinda a aikin su, amma ash Sheikh farfesa Ali isah pantami yayi ƙarin haske ga masu wannan gurgun tunani inda hake cewa.

Tattaunawa da ankayi da sheikh farfesa Ali Isah Pantami akan irin abubuwan da yake irin aikin gwamnati da yayi a baya da kuma aikin wa’azi da karantar wa

Jahilci Ko Son Rai Ke Sa Wasu Cewa Bai Kamata Malamai Su Shiga Siyasa Ba - Prof Pantami
Jahilci Ko Son Rai Ke Sa Wasu Cewa Bai Kamata Malamai Su Shiga Siyasa Ba – Prof Pantami

“Ayyukan da nake kala kala ne irin na shugabanci haryanzu shi chancellor ne na jami’ar kasar sudan, na biyu a nan Nijeriya akwai jami’o’i da nake masu ruwa da tsaki a cikin su, sa’a nan ina karantawa a jami’o’i guda biyu a nan Nijeriya dukkanin su iya ne kyauta ne ba biyana ake yi ba.

Advertisment

Sa’a akwai hanyoyi na neman abinci da za’a rufawa kai asiri irin aikin mu na ICT, ko digital economy, da sauran harkokin da suka shafi yanar gizo wanda muna da abokan aiki irin a USA, saudi arabia da dai sauran su hausawa kance sana’a goma maganin baccin rana.- inji sheikh pantami

Mai tambaya yayiwa malam tambaya ya dace da mutum mai ilimi da addini da zamani ya shiga shiyasa domin har masoyanka suna kira da hakan

“To ae na riga na shiga siyasa domin duk mutumin da yayi aikin gwamnati har yakai minista ai bai isa yace bai shiga siyasa ba., akwai lokacin da bana shiyasa siyasa a lokacin bata kama ba, a lokacin da na zauna a bauchi daga karantarwa a jami’ar ATBU daga karantarwa sai limanci ban shiga siyasa ba, to amma idan girma ya kama kana da wasu abubuwa da mutane zasu amfana zaka shiga .

Misali ga a lokacin da nake karantawa a saudi arabia shugaban kasar mu buhari shiya umurni in dawo Nijeriya a lokacin yace madina na dawo ya sani a DG bayan shekara ukku ya sanya ni a minista idan ka rike wannan mukamai shine “political appointment” kaga ai shikenan magana ta tabbata.-inji Sheikh pantami.

“Wadanda suke ganin masu addinin musulunci bazasuyi aikin gwamnati ko siyasa ba gaskiya son rai ne ko jahilci ne, amma in ba haka ba ita kalma “Siyasa” kalma labarci ne kuma daga hadisi aka same ta.”

Ga hirar nan ku saurari cikakken bayyani.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button