Labarai

Barrister Abba hikima yayi tambihi kan ‘copy’ na hukunci daukaka kara “Appeal” na jihar kano

Lauya Abba hikima yayi tambihi aka copy da anka samu ana cece kuce akan nuna cewa tabbas abba kabir Yusuf yayi nasara wanda ya fadi fahimtarsa a matsayin na lauya.

A fahimtata wannan kuskure ne kotun daukaka kara tayi. Da wuya ka dauki hukuncin kotu ka karanta baka samu kuskure ba. Ba’a zabar wani bangare na hukunci a karanta a manta da sauran. A wannan hukuncin duka sauran bangarorin hukuncin ya nuna AKY bai yi nasara a Appeal ba.

Saboda haka, ba za’a dauki wata sadara daya a tsaya a kanta ba. Wannan abu sannane ne a doka kuma doka tayi tanaji na a abunda ake kira “Slip Rule”wanda shine idan an samu kuskure ko tuntuben alkalami a hukunci, to kotu na iya gyara wannan kuskuren musamman idan ma’anar hukuncin ta bayyana.

Saboda haka, gara a bawa ainihin dalilan daukaka wannan kara muhimmanci fiye da wannan.

A wani rubutu da ya wallafa bayan wannan da ya kawo ya kara da cewa.

Ban san gaibu ba kuma bana cikin lauyoyin AKY ko NNPP, amma ina tabbatar muku sai sun daukaka kara. Daukaka kara kuma wanda baiyi nasara ba shi yake yi. Saboda idan za’a daukaka kara, hujjoji da nuazarin kotu ake kalla ba sadara daya ko biyu ba. Shi yasa dalilian daukaka karar AKY daga tribunal zuwa kotun daukaka kara suka zarce 40.

Ta yaya zaka samu dalilai 40 idan pagi daya zaka yi lakari da shi. Sannan sauran alkalan wannan kotun fa duka sun kori appeal din sun tabbatar APC ce taci. Ta yaya zaka makale a pagi na daya? Amma idan ba’a yadda ba, ga fili ga mai doki. A bari kwana 21 su wuce ba’a daukaka kara ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button