Labarai

Kotu za ta yanke hukunci kan shari’ar zaben Gwamnan Nasarawa gobe

Advertisment

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta sanya ranar Alhamis domin yanke hukunci kan shari’ar zaben gwamnan jihar Nasarawa.

Gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar APC ne ya shigar da kara kan hukuncin kotun tirabunel da ta ce ba shi ya lashe zaben ba inda ta bayyana David Ombugadu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kotu za ta yanke hukunci kan shari'ar zaben Gwamnan Nasarawa gobe
Kotu za ta yanke hukunci kan shari’ar zaben Gwamnan Nasarawa gobe

Hukumar zaben Nijeriya INEC ta bayyana Sule a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar ta Nasarawa da aka gudanar a ranar 18 ga Maris din shekarar nan, sai dai Ombugadu ya garzaya kotu inda ya kalubalanci nasarar ta Sule.

A cewar INEC, Sule ya samu kuri’u 347,209 inda ya doke abokin hamayyarsa wanda ya samu kuri’u 283,016.

 

Wani labari : An dakatar da Khadija amai numfashi daga harka fim

 

Yanzu nan majiyarmu ta samu labarin kamar yadda nasara radiyo ta ruwaito yanzu nan hukuma tace fina finai ta dakatar da wata jaruma daga Masana’atar Kannywood.

“Hukumar tace finafinai da dab’i ta jihar Kano karkashin jagorancin Abba El-Mustapha ta dakatar da jaruma Khadija Mai Numfashi har tsahon shekaru 2 daga fitowa a kowanne fim, sakamakon wani bidiyo da ta saki, kuma ta gagara zuwa ta kare kanta
tsawon kwanaki goma sha daya.”

Wannan hukuncin ya biyo bayan ta fitar da wani bidiyo da hukumar ta nemi tazo ta kare kanta amma ta gagara zuwa.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button