Labarai

Labari Mai Dadi ! Ƙasar Saudiyya Ta amince a koma Aikin Umrah

Saudiyya ta sanar da za ta kyale mazauna ƙasar su gudanar da ayyukan ibada na Umrah bayan ta dakatar da komai na tsawon watanni.
Hukumomin ƙasar sun ce dag baya za su kyale maniyyata dag ƙasashen waje su shiga ƙasar domin gudanar da ibadar wadda ta ke da muhimmanci ga Musulmin duniya, sai dai za ta ƙayyade yawan maniyyatan da yawan ƙasashen da za ta bari su shiga ƙasar.
Maniyatta da ke cikin Saudiyya na iya yin Umrah daga ranar 4 ga watan Oktoba, inda maniyattan da ke ƙasashen ƙetare kuwa sai sun jira zuwa ranar 1 ga watan Nuwamba kafin su sami izinin shiga ƙasar.
Bbchausa ta ruwaito,ma’aikatar Aikin Hajji ta Saudiyya ta kuma bayyana cewa idan annobar korona ta gushe, za ta kyale dubban maniyatta daga ko’ina a duniya su ci gaba da ziyartar biranen Makkah da Madin domin gudanar da ibadunsu.
Musulmi na iya yin ibadar Umrah a duk lokacin da suka so, ba kamar aikin Hajji ba da ake iya yi sau ɗaya kawai a kowace shekara.
Miliyoyin Musulmi daga sassan duniya kan tafi Saudiyya a kowace shekara domin sauke wannan muhimmiyar ibada da ke ta biyu ga aikin na Hajji a daraja.
Bbchausa ta ƙara ta kara da cewa,tun dai a watan Yulin bana hukumomin Saudiyya suka ɗauki matakai domin daƙile bazuwar annobar korona, A bana mutum 10,00 ne kawai suka yi aikin Hajji a maimakon kimanin miliyan biyu.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button