Labari mai daɗi: Jami’an tsaro na KSCWC sun tarwatsa dabar kasurgumin dan bindiga Ɗangote, sun hallaka yaransa 15 a jihar Katsina


Jami’an tsaron al’umma ƴan-sakai “Katsina Community Watch Corps” na ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina sun tarwatsa dabar kasurgumin ɗan ta’adda Ɗangote, inda suka hallaka yaransa 15 a wani harin kwantan ɓaure wanda suka farmaki ƴan bindigar.
Katsina Reporters ta samu cewa, Jami’an KSCWC sun ci galabar ƴan bindigar ne, a wani harin kwantan ɓauna da suka kai masu a daji, inda suka fatattakesu tare da hallaka ƴan bindiga 15 da kuma ƙwato bindiga ƙirar AK-47 daga hannunsu.
Ƙaramar hukumar Batsari na daga cikin garuruwan da suke fama da matsalar tsaro a jihar Katsina inda ake ka-she mutane tare da yin garkuwa da jama’a zuwa daji don neman kuɗin fansa.
Wani labari : Shugaban Bankin Access Bank na Najeriya Herbert Wigwe shi da matarsa da ɗansa sun yi haɗarin jirgin sama sun mutu gaba ɗaya a ƙasar Amurka
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a kusa iyakar California zuwa Nevada a sararin samaniya.
Kamar yadda New York Times ta rawaito ta ce babu wanda ya rayu cikin fasinjoji dake cikin jirgin.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





