Babu dalilin da zai sanya a cirewa gwamnan Kano kuri’u 165,000 a Kotu – Femi Falana
Babban lauya mai kare hakkin dan Adam a Nigeria, Femi Falana, ya soki hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke na soke nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, tare da bawa Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC.
Lauyan ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da Gidan Talabijin na Channels a ranar Juma’a, inda ya ce, watsi da kuri’u 165,000 kan rashin yin tambari bai dace ba, bai kamata Alƙalai su hukunta masu kada kuri’a kan kura-kuran da INEC ta yi ba.
“Ba za ku iya hukunta masu kada kuri’a kan kurakuran INEC ba. Abin da ya faru kwanan nan kenan a Kano, inda aka ce kuri’u 65,000 da jami’an INEC ba su samu ba.
Muna rokon alkalan mu da su rungumi adalci, adalci mai yawa, ta yadda ba za ku iya hukunta masu kada kuri’a kan kurakuran INEC ba.”
Wani labari na daban : Ganduje ya bar mana bashin kuɗi sama da Naira Biliyan 500 – Gwamnatin Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta yi zargin cewa tsohon Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya bar mata gadon bashi na sama da Naira biliyan 500.
Mataimakin Gwamnan Jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya bayyana hakan yayin taron shiyyar Arewa maso Yamma na jam’iyyar NNPP a Kaduna, ranar Juma’a.
Aminiya ta rawaito cewa, ya ce suna hasashen idan suka kammala tantance yawan bashin, zai iya haura biliyan 500 din, kuma hakan na kawo wa tafiyar da gwamnatin jam’iyyarsu tsaiko a Jihar.
“Mun karbi mulkin Kano ba mu tarar da komai ba sai bashi. Da farko bashin biliyan 300 ne, amma yanzu ya fara dosar biliyan 500, kuma har yanzu muna ci gaba da tattarawa. Da zarar mun kammala aikin tattarawar, za mu sanar da ’yan Najeriya, musamman Kanawa ainihin yawan bashin domin su san halin da ake ciki,” in ji shi.