Labarai

Motar Naira miliyan 130 da za a baiwa kowanne ɗan majalisar wakilai ta kusa karasowa Nijeriya

Majalisar wakilai ta tabbatar da cewa majalisar dokokin kasar na shirin sayo tare da raba mota kirar Prado jeep, wacce kuɗin ta ya kai Naira miliyan 130 ga ko wanne dan majalisa.

Majiyarmu ta samu labarin daga jaridar Daily Nigerian Hausa Kakakin Majalisar Wakilai, Rotimi Akin ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja a daren Lahadin juya, inda hakan ya zo ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke kokawa kan matsalar tattalin arziki.

Akin ya ce shirin ya yi dai-dai da dokokin sayan kayayyaki da ake da su, inda ya ce al’ada ce da majalisar ta saba yi tuntuni.

Ya ce za a raba motocin ne ga ƴan majalisar domin gudanar da ayyukansu na kwamitoci, inda ya kara da cewa motocin ba kyauta ba ne.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button