Babbar Magana! ‘Yar fim ta sha alwashin zama shugabar kasar Najeriya
Tonto Dikeh, ‘yar fina-finan Nollywood, ta bayyana wannan buri na ta a shafin ta na Instagram a ranar Talata.
A shafin ta na Instagram.
Akwanakin bayane Tonto ta bayyana soyayyar da ta yi da wani attajirin matashin ɗan siyasa, mai suna Prince Kpokpogbi ɗan asalin Jihar Delta.
Tonto Dikeh wadda ‘yar asalin Jihar Ribas ce, ta kuma sanar cewa kuma ta bayyana hotunan na ta a shafin Instagram masu nuna cewa a wata babbar makaranta ce aka yi su.
Ta bi hotunan ta rubuta: “To ni dai na koma makaranta, saboda na ƙudiri aniyar zama shugaban Najeriya”
Bata dai bayyana sunan makarantar ba. Sai da ko a cikin 2020 da mujallar Ovation tayi hira da ita, ta ce ta na sha’awar zama sanata, kuma wataƙila ta fara daga matakin na sanata a 2023, domin share hanyar zama shugaban ƙasa.kamar yadda zinariya na ruwaito.
Mezakuce?