Cire Tallafin mai: NLC ta yi barazanar yajin aikin sai-baba-ta-gani a ƙarshen wa’adin kwanaki 21
Kungiyar Kwadago ta Ƙasa, NLC, ta yi barazanar fara yajin aikin sai-baba-ta-gani, idan har gwamnatin tarayya ta gaza biyan bukatun ta a karshen wa’adin kwanaki 21 da ta ɗauka.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa kungiyar ta bayar da wa’adin ne a ranar 1 ga watan Satumba kan wani jinkiri da gwamnati ta yi na aiwatar da matakan da suka dace domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Daga bisani sai kungiyar ta shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyu tsakanin 5 zuwa 6 ga watan Satumba domin nuna cewa da gaske ta ke.
Sai dai da ya ke magana yayin wata tattaunawa da jaridar Punch a jiya Talata, mataimakin babban sakataren kungiyar ta NLC, Christopher Onyeka, ya ce barazanar yajin aikin ya biyo bayan halin ko in kula da gwamnati ke yi na biyan bukatun ma’aikatan Najeriya.
Ya bayyana cewa matakin yajin aikin, wanda zai iya farawa kowace rana a mako mai zuwa, zai haifar da dakatar da ayyukan kasuwanci da tattalin arziki a fadin kasar nan har sai-baba-ta-gani.
Sakataren kungiyar ta NLC ya kara zargin gwamnatin tarayya da nuna halin ko-in-kula daga tattaunawa a tsakaninsu.
Ya ce: “Mun aika da wasikar zuwa ga Gwamnatin Tarayya a ranar 1 ga Satumba, 2023, don haka zuwa ranar 22 ga Satumba, 2023, wa’adin kwanaki 21 zai kare.
“Mun bayyana karara cewa Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da tattaunawar mu; gwamnatin ta daina tattaunawa da ’yan Najeriya kuma babu wata tattaunawa ta gaskiya da ke gudana.
“Shugaba Bola Tinubu ya yi wa ‘yan Nijeriya alkawarin shi kadai a gidan talabijin da Shugaban NLC, Joe Ajaero, cewa zai sake fasalin kwamitocin, amma bai yi haka ba, kuma tun a wancan lokaci kwamitocin ba su hadu ba kuma babu tattaunawar da ke gudana. Halin da ake ciki yanzu, NLC ba ta tattaunawa da gwamnati,” in ji Mista Onyeka