Labarai

Hatsarin ‘Yar Kwangilar Yahudawa Aisha Yesufu Ga Rayuwar Musulmai (Hotuna) ~ Datti Assalafy

 
Duk wani Musulmin kirki da ya san wacece Aisha Yesufu har yake kaunarta ko yake goyon bayanta matukar ya san muguwar akida da muguwar manufa da take tattare da shi sai yayi nadama ko ya tsani kanshi
Don Allah ‘yan uwa Musulmi ku nutsu da kyau ku karanta wannan sakon har karshe wanda ‘dan uwa Ibn Adam ya bincika mana akan wannan mata ‘yar gwagwarmayar kare ‘yancin yahudawa da kungiyoyin ‘yan Luwadi da Madigo na duniya
Wani ya tambaye ni wai menene hujja ta na adawa da wannan matar, Maganar gaskiya akwai dalilai masu karfi wanda ya sa bana yinta, a yau Musulmai sai mun zama masu lura sosai da ababen da suke faruwa, in ba haka ba za’a cutar da mu duniya da lahira
Daga cikin Hojjojin da ya zama wajibi duk wani Musulmin kirki ya kamata ya tsani wannan matar shine:
(1) Tana sanye da hijab” : Duk da tana sanye da hijabi, hakan be hanata yin abubuwa wanda suka sabawa shariah Musulunci ba, hakan sai ya sa Jahilai da gamagarin mutane su dauke ta “jaruma mai hijabi” harma ta zama abun koyi wa na bayanta musamman mata masu tasowa. Saboda ta shahara kuma tana sanye da hijabi, a dauka ayyukan ta sunyi daidai da abinda musuluncin ya hukunta. Hakan kuma na da illa matuka ga Al’ummar mu.
Ni ba ina magana ne kan zanga-zanga ba, sam ba shine makasudin magana ta ba, duk wanda ya san ta a shafin Twitter ya san irin tsiya da take rubutawa wanda yaci karo da addinin Musulunci karara.
2. Tana da akidar Liberalism, wato tana da akidar cewa abar mutane suyi abinda suke so ko da abin ya saba wa shari’ar Allah, hakan ya sa tayi rubutu a shafin ta na Twitter take magana akan bada ‘yanci wa kungiyoyin ‘yan Luwadi da Madigo da masu zina da Dabbobi na duniya, wato kungiyar “Lesbian, Gay, Bisexual, and Transgender” (LGBT)
Tayi maganganu cewa mutane na da ‘yanci suyi auren jinsi, namiji ya auri namiji, mace ta auri mace, harma take kokarin nuna cewa a jihar Kano akwai masu aure jinsi da jinsi kuma ana zaune dasu lafiya kuma ana mu’amala dasu yanda ya kamata, don haka indai zasu zauna to a basu ‘yancin auren juna kawai.
To wannan maganar ma ko a constitution babu ‘yancin auren jinsi balantana a tsarin Allah (SWT) da MazonSa (SAW)
3. Tana tare da ArewaMeToo, Duk irin tsiya da da wannan kugiyar take neman ta shuka a arewa, wannan matar tana goyon bayan wannan kungiyar saboda akidar su daya.
Cikin wani sakon Twitter da ta rubutu ta goyi bayan cewa ArewaMeToo suyi magana akan bada ‘yancin Madigo da Luwadi (Lesbianism Homosexuality) saboda akwai irin wadannan mutane a Arewa da dadewa, kuma ba’a cin zarafin su, kuma ba’ayi yinkurin dakatar dasu ba.
Allah Yace: Ku taimaki juna a kan aikin kwarai da takawa, Kuma kada ku taimaki juna akan zunubi da zalunci. Suratu Ma’idah (Q5:2)
4. Cikin ‘yan kwanakin nan da aka yanke wa wannan mawakin hukuncin kisa a Kano wanda ya zagi Manzon Allah (SAW) Aisha Yesufu ta nuna rashin amincewar ta akan hukuncin.
A takaice tana da mummunar akida, kuma a zato na Mutum me irin wannan akidar baya bukatar a yaba masa harma ya kai ga ana tallata shi a matsayin jarumi, harma wasu suna cewa jarumtar ta ya samo asali ne daga ainihin me sunar wato Nana Aisha (ra) matar Manzon Allah (SAW) wannan ko shakka babu abin takaici ne sosai a kwatanta wannan bayahudiya da darajar Nana Aisha kamar yadda wani babban ‘dan siyasa a jihar Niger Umar Nasko ya wallafa a shafinsa na facebook saboda cin mutunci
Naji mamaki matuka da naga wasu Musulmai suna daukan ta wata jaruma me sanye da hijabi, har suna sa hotunan ta a matsayin DP dinsu, kamar Mutane sun manta ko kuma abin duniya ne ya fi damun su.
Zanga-Zanga ba wani abin jarumta bane, kowa ma zai iyayi, alakar ka da mutum da sonsa da kake yi ya samo asali da yanda mutum yake da kyakkyawar alaka tsakaninsa da Allah da ManzonSa ne, wannan shine ma’auni
Wannan itace jarumar ka wanda kake ganin tayi abin gwaninta ko? , tun da wuri ya kamata ka fahimta ina aka dosa, kada ta zama abin koyi gun ‘ya’yanka ko yaran gidan ku, su taso suna goyon bayan kungiyoyin ‘yan Luwadi da Madigo, domin babu mai goyon bayansu sai wanda yake cikinsu
Yana daga cikin hanyoyi da yahudawan duniya suke bi su cutar da Al’ummar Musulmi shine a samu irin wadannan mutane a sa su shahara, ko kuma idan sun shahara a mayar dasu kamar wasu jarumai har sai ya kai munzilin da an yarda dasu, hakan sai ya basu damar cigaba da tallata mummunar akidarsu, da sunan cewa su jarumai ne na gwagwarmaya da kare ‘yanci na dan-Adam.
Nayi wannan rubutu ne da niyar farkar da zaciyoyin Musulmai don su fahimta cewa kamar yanda bature ke fadi “ not all that glitters is Gold”.
Kalli irin abubuwan da tayi wallafawa a shafinta na twitter.

Rubutawa : Datti Assalafy
Allah Ya sa mudace.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button