Kannywood

Mustapha Nabaraska yayiwa hukumar tace fina finai martani Mai zafi kan dakatar da komai a harka fim

Gwamnatin Kano Na Iya Fita Daga Raina Idan Aka Cigaba Da Abinda Ake Yi Wa ‘Yan Fim Game Da Rijista Cewar Nabraska

Mustapha Nabaraska ya bayyana hakane wata fira da freedom Radio kano ya zanta daji domin jin ta bakinsa wanda a shekarar jiya ne shugaban hukumar tace fina finai abba elmustapha yace sun tsayar duk wata harka ta tsaya chak har sai nan da sati biyu idan an kamala sabunta lasisi ko kuma yin rigista.

Jarumin ya kuma bayyana cewa su kansu suna maraba da nuna goyon baya idan za a yi gyara, babu wanda ba ya son gyara, amma ana duba mafitar al’umma ne.

Mustapha Nabaraska yayiwa hukumar tace fina finai martani Mai zafi kan dakatar da komai a harka fim
Mustapha Nabaraska yayiwa hukumar tace fina finai martani Mai zafi kan dakatar da komai a harka fim Hoto: Freedom Radio kano

“Kai wannan ae zance ne taya za’a ace an tsayar da masana’anta Allah ya tuba daman saboda sana’ar ba yinta akeyi ka’in da na’in ba saboda alumma komai ya riga ya tsaya kasar ma, bama iya na jiha ba taya za’a ce an dakatar idan ka dakatar me zaka baiwa mutane kafin su dawo su cigaba da yi.

Me ka tanadar musu Sa’a nan ina sana’ar take , minene hujjar ka na dakatarwa akwai abinda ake dakatarwa domin ta fuskar gyara amma kuma ana kallon wane hali alumma zasu samu kansu a ciki.

Nabraska kada ace ko baku so ayi gyara ne?

” Mukam ae muna goyon bayan gyara ita al’umma idan ba’a zaman gyara ae akwai kuskure, ana duba maslaha al’umma ne ae sai a fito ayi gyara a dubi minene abu mafi sauki ko kuma mafi girma a cikin al’umma.”

Jarumin ya ce “Allah Ya sani muna son gwamnatin nan amma a sanadiyyar wannan abin ni a matsayina na ɗan Kannywood gwamnatin nan tana iya fita daga raina sanadiyyar abinda za a yi wa ƴan uwana tunda na san ba su da shi, wadanda suke da shi ƙalilan ne.

Mutsapha Nabraska ya bayyana abubuwa sosai wanda suke ganin sam ba’a dauko hanya mai bullewa ba.

Ga hirar nan ku saurara kuji.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button