Labarai

Ƴan Kwankwasiyya Ƴan Ta’adda Ne – Alƙali Justice Anya

Wato abinda hausawa kance tsugune bata kare ba domin daya daga cikin alkalan da sunka yanke hukuncin zaben jihar Kano yaji zafi da radadin irin yadda wasu dake cikin gwamnatin Abba Kabir Yusuf sunkayi barazana wajen ganin sai cewa duk wani alkali da yayi musu ba dai-dai kashin sa zai bushe.

Shafin sarauniyar news sun wallafa wannan rubutun a shafinsu na sada zumunta inda suke fadin abinda alkali anya ya fadi akan yan kungiyar kwankwasiyya.

Ƴan Kwankwasiyya Ƴan Ta'adda Ne - Alƙali Justice Anya
Ƴan Kwankwasiyya Ƴan Ta’adda Ne – Alƙali Justice Anya Hoto : Facebook

Ɗaya daga cikin alƙalai huɗu da suka saurari ƙarar zaɓen gwamnan jihar Kano, wato Justice Benson Anya, ya kwatanta ƴan Kwankwasiyya a matsayin fusatattu kuma ƴan ta’adda sakamakon barazanar da wasu suka yi na ɗaukar matakan ladabtarwa akan alƙalan.

Jim kaɗan bayan furta wannan kalaman tunzuri gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusif ya ɗauki matakin cire mutum biyu daga muƙaman su, sannan ya nesanta jam’iyyar su ta NNNP da wannan kalamai.

Sai dai da dukkan alamu wannan bai sanyaya zuciyar alƙali Benson Anya ba, domin ko a kwafin takardar yanke hukunci da ya soke zaɓen Abba aka ba wa Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC, sai da ya bayyana ƴan Kwankwasiyya a matsayin fusatattu kuma ƴan ta’adda.

Lamarin da ya janyo hankalin wasu mutane da dama har aka riƙa sukar sa tare da cewar, ba daidai ba ne ya sako wannan lamari cikin ƙumshin shari’ar zaɓen gwamna.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button