Labarai

Yanzu yanzu: Barawo ya yi awon gaba da zunzurutun kudi dala 75,000 a hedkwatar APC

Abuja – An shiga rudani a sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa a ranar Laraba, 27 ga watan Afrilu, lokacin da zunzurutun kudi har kimanin naira miliyan 43 ya yi batan dabo.

An tattaro cewa an ruguza babban rumfar da a karkashinsa ake siyar da fom din takara ba tare da wani cikakken bayani ba.

Jaridar legit ta rahoto cewa jam’iyyar ta yanke shawarar amfani da manyan rumfunar da aka kafa ne saboda aikin gyare-gyare da ake yi a ainahin ginin sakatariyar.

An rahoto cewa kudi dala 75,000 ne ya yi batan dabo a yayin da ake turereniya wajen shiga harabar jam’iyyar.

Majiyar ta ce:

$75,000 ne. kun san akwai turereniya a wajen sakatariyar lokacin da yan takara da magoya bayansu ke kokarin shiga ciki.
“Lokacin da damin kudin ya fadi, sai aka neme shi aka rasa a cikin kyaftawan ido. Zuwa lokacin da aka sanar da jami’an tsaro tuni barawon ya arce da takardar kudin.”

Sakatariyar jam’iyyar dai ta cika ta tunbatsa yayin da yan takara ke karbar fom din takarar kujerun shugabanci.

Daruruwan magoya baya sun taru a wajen Buhari House domin karfafawa yan takarar da suke goyowa baya gwiwa a hanyarsu ta shiga harabar.

Siyar da fom da aka yi na ranar Laraba ya nuna karara cewa ba lallai ne harabar jam’iyyar ya dauki shirin na kimanin makonni biyu ba.

The Eagle ta rahoto cewa ana kan tattaunawa domin mayar da shirin zuwa wani waje na daban.

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, an jiyo jami’an jam’iyyar suna tattaunawa domin mayar da shirin zuwa babbar cibiyar taro na kasa, Abuja.

Sai dai kuma, majiyoyin jam’iyyar sun bayyana cewa kudin da ya bata bai da alaka da kudaden da aka siyar da fom din takara domin ana sanya ran masu takara za su tura kudin ne a asusun bankin da aka tanada don haka kafin su karbi fom dinsu a Buhari House

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button