Kannywood

Soyayyar Rakiya Da Breaker Ni GANAU Ba Jiyau Ba – cewar wani matashi ya bada labari mai ban mamaki

Da fari dai ban so na saka baki na akan maganar nan ba kwata-kwata, saboda a wajena, ba kowane batu ne ya ke buƙatar tankawa ba. To amma abubuwa biyu sun ja hankali na ƙwarai da gaske. Abu na farko shi ne tausayin da Rakiya ta bani, ta kuma bawa mutane da yawa bayan kallon hirar su da na yi da Hadiza Gabon. Sai abu na biyu yadda na ga wasu na alaƙanta cewa wannan masoyin ba wani ba ne illa Hamisu Breaker. Mu’azu suleiman sa’eed ne ya bada wannan labarin a shafin na facebook

Wannan gaɓar ta biyu ta yi daidai da tunanina bayan kammala kallon hirar da muka yi tare tawa masoyiyar da bamu wahalar da juna ba????. Ina gama kalla, nace mata, Allah ya sa ba BREAKER ta ke nufi kuwa. Ummu Hanan tace anya kuwa?Soyayyar Rakiya Da Breaker Ni GANAU Ba Jiyau Ba - cewar wani matashi ya bada labari mai ban mamaki

Mu dawo maganar mu. A ƙarƙashin wannan gaɓa ta biyu ina da abubuwan faɗa dozin guda kamar haka:

1. Ban yi wannan rubutun domin aibata wani ko bawa wani kariya a cikin su biyun ba. Illa dai kawai na ɗan san wani abu dangane da alaƙar su biyun.

2. Hamisu maƙobcin mu ne a unguwar Dorayi, domin gida ɗaya ne tsakanin mu da gidansu, don haka tamkar ƙani ya ke a wajena tun bai kai shekara biyar a duniya ba. Bayan kasancewarsa maƙobcin kuma tamkar ƙani, Hamisu ɗalibi na ne na tsawon shekaru kafin yai nisa a harkar waƙa, domin kuwa har ya fara waka yana koyar karatu a wajena.

3. Ban san abin da ya fara haɗa Hamisu da Rakiya ba, amma na tabbatar cewa Rakiya ta yiwa ko kuma tana yi wa Hamisu so maras misaltawa, domin kuwa ta kan zo ta wuni a gidansu tare da mahaifiyar sa, su yi hira, ta taya ta aiki, kuma ta raka ƙanwarsa Khadija duk inda aka aketa (kanti, siyo kayan miya da sauransu), duk da kasancewar matsayinta na tauraruwar fim (ko nace celebrity).

4. Ba sau ɗaya ba, ba kuma sau biyu ba, duk lokacin da na shiga gidan su Hamisu na sameta (Rakiya) ko suka fito da Khadija ko da shi Hamisu, in har Hamisu zai gaisheni to sai ta rusuna take gaishe ni. Saboda duk wanda ta fahimci yana da wata ƙima ko influence akan Hamisu tana girmama shi.

5. Ba ni kaɗai ba, duk waɗanda suke rukunin gidanjenmu sun saba da ganinta domin a wancan lokacin ɗaiɗai ne ranekun da bata gidan su Breaker (ko da baya gari).

6. Tambayar a nan shi ne, shin Hamisu Breaker ya taɓa soyayya da Rakiya?

7. Ba zan iya amsa tambayar kai tsaye ba, amma tun a wancen lokacin, abin da mafi yawan mu muka fahimta shi ne Rakiya ke neman soyayyar Hamisu Breaker. Kuma ina da dalili.

8. Na taɓa tattaunawa da shi a kan alaƙarsa da Rakiya, musamman akan zuwan da ke gidansu na rashin dacewar hakan. A lokacin ya bani amsar cewa tana sonsa ne, shi kuma gaskiya bai aminta ba. Ta kan zo gidan har ta tafi basu haɗu ba, domin ita tana zuwa wajen mahaifiyarsa ne da niyyar kamun ƙafa. Don haka ba yadda zai iya hana ta zuwa, saboda ya faɗa mata bata ji ba. Mun yi makamanciyar wannan maganar da mahaifiyar Hamisu watarana, kuma amsar da na samu bata ci karo da abin da Hamisu ya faɗa min ba.

9. Kamar yadda na ji (daga wasu abokansa) cewar akwai waƙoƙin da sukai tare da Hamisu wanda ita ta ɗau nauyin su, ta biya shi, ta kuma roƙe shi su yi video ɗin waƙar tare.

10. A lokacin da duk waɗannan abubuwan suke faruwa, Hamisu bai yi shura an san shi a ko ina kamar yanzu ba. Don haka in dai ya tabbata shi ne wanda Rakiya ta ba da labari, to tabbas ba ɗaukaka ce ta raba su ba, tun farko ta gino soyayyar ta ne da tubalin toka, ko kuma son maso wani.

11. Na iya tunawa a cikin hirarta akwai inda tace “Ya yi min duk wani abu da ya kamata na rabu da shi, na ma manta da shi a rayuwa ta, amma ban rabu da shi ba”. Idan har ya tabbata Breaker ne take nufi, to tabbas ni kai na naga dagiyar ta a irin yadda tun yana kulata, har ya zama yana sha mata ƙanshi, da mu’amalar da za ta rabu da shi ɗin amma bata dena ba.

12. A taƙaice, ba ina ganin laifin Rakiya ba ne, domin sha’anin so ya fi ga haka. Haka kuma ba ina kare Hamisu ba ne, amma ni ganau ne cewa tun ba a san Hamisu Breaker sosai ba, ya nuna rashin karɓar soyayyar Rakiya, don haka rabuwar su ba ta da alaƙa da matsayin da ya samu a rayuwa.

Ina ƙara tausaya mata matuƙar gaske, ina kuma yi wa dukkan masoya fatan Allah ya haɗa su da masoyansu na gaskiya (a cikin aure).

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button