Daga Karshe Hamisu Breaker Ya Fadi Gaskiyar Abinda yake tsakaninsa da Rakiya Musa
Tun bayan fallasar da wani faifayin Bidiyo a kafafen sadarwa wanda ke nuna jarumar Kannywood Rakiya Musa tana sharar kuka bayan ta bayar da labarin wani bangare daga cikin labarin Soyayyar ta, aka ta baje kolin raayoyin kan batun.
A tashar jaruma Hadiza Gabon aka yi hira da jaruma Rakiya wanda ta dunga sharar kuka kan yadda tsohon saurayinta yayi layar zana lokacin data fi bukatar sa.
Majiyarmu ta samu wannan labarin daga Dimokuraɗiyya a page dinsu Bata bayyana sunan saurayin ba, sai dai yan soshiyal Midiya suna bayyana mawaki Hamisu Breaker a matsayin wanda suke hasashe a matsayin saurayin Rakiya.
Sai dai Breaker ya karyata batun da cewar babu ruwan Gizo bare Qoqi, hasalima babu wata maganar soyayya a tsakanin shi da Jarumar.
“Assalamu alaikum masoyana tare da fatan kun sha ruwa lfy dazu wasu daga cikin masoyana suka ja hankali akan wannan batun da yake ta yawo cewa Rakiya Musa ƴar Asalin Niger wai dani tayi soyayya kuma har na juya mata baya Sam Sam wanna maganar ba haka take Hasali ma ni babu wata alaƙar soyayya tsakanin mu sai dai Mutunci”.