Kannywood

Wannan Bidiyon Ya jawowa Jaruma Maryam babban yaro cece kuce

Fitacciyar jarumar Kannywood Maryam Gidado da aka jima ba’a jin duriyar ta ko kuma ganin fuskarta a cikin finafinai ta wallafa wani fefen bidiyo.

Jarumar ta saki bidiyon ne a shafin ta na sada zumunta na Tiktok,ta nunawa duniya yadda ake yi mata Kwalliya bayan hatsaniyar data faru da ita da masoyanta, wadanda suke ganin bata da kudin siyan kayan Kwalliyar ne ko kuma ta kare mata.

Jarumar ta nuna bidiyon cike da annushuwa bata tunanin maganganun da sunje su dawo.

Wannan Bidiyon Ya jawowa Jaruma Maryam babban yaro cece kuce
Wannan Bidiyon Ya jawowa Jaruma Maryam babban yaro cece kuce

Sai dai a kasan bidiyon,mutane da dama sunyi mamaki,wasu har suna fadin wai babu ta yadda mace zata dinga yiwa mace “yar uwarta Kwalliya ne a Kannywood dole sai Maza?

Haka da makamantan su mutane sukaci gaba da bayyana ra’ayoyin su.

Ba tare da dogon Turanci ba,zaku iya kallon cikakken bidiyon anan kasa,kada ku manta ku bayyana mana ra’ayoyin ku akan hakan.

Kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su, mungode!

Ga bidiyon nan.

 

Hausaloaded ta tattaro martanin mutane a karkashin wannan posting din.

@Muhammad Dauda.:Waisu kannywood ƙa’idane namiji shine yakeyin kwalliya?

@Laila:Rashin sanin addinine

@Khadijatulkubrah:Nimadai abinda nakasa ganewa kenan haryanzu

@alikwabo:Kawai kin zauna kin mikawa dan hamsin kai ya daura miki kallabi kuma kin nunawa duniya dole ko a samu matsala

@Abdulrashid:Shin Wai acikin tsare-tsaren kannywood wace doka ce tace Dole Sai namiji ne zaiyima mace kwalliya ne?

@diksarsadeeq:kutt!! yanxu kuma daga anyi magana sai kace kowa da sana’arsa hanyar cin abincika ne. kafin duniya tayi atishawar tsaki daku Allah ya shiryeku.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button