Labarai

Ganduje ya kori Kwamishinan Horkokin Addini, Baba Impossible

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kori Kwamishinan Horkokin Addini, Dakta Muhammad Tahar Adam, wanda a ka fi sani da Baba Impossible. Daily Nigerian Hausa na ruwaito

Ganduje ya kori Kwamishinan Horkokin Addini, Baba Impossible
Ganduje ya kori Kwamishinan Horkokin Addini, Baba Impossible

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da Muhammad Garba, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin gida da ya fitar a yau Asabar a Kano.

A sanarwar, Garba ya ce korar ta nan-take ce.

Ya ƙara da cewa korar ta biyo bayan wasu halaye marasa daɗi da Baba Impossible ke nunawa a matsayin sa na mai riƙe da ofishin gwamnati, inda ya ƙara da cewa kalaman mara sa dacewa da ya ke furtawa na cikin dalilan da ya sa Ganduje ya saita wa Kwamishinan hanya.

A cewar Garba, an gano cewa Baba Impossible na gudanar da harkokin ofishinsa a matsayin wani kasuwanci sannan kuma ya rage ranakun zuwa ofis na ranaku biyu, Laraba da Juma’a.

Malam Garba ya ƙara da cewa bayan laifin gudanar da ofishin sa ba tare da tuntuɓa ba, Baba Impossible ba ya biyayya ga Gwamna Ganduje.

Ya ƙara da cewa tuni gwamnan ya aike da sunan Dakta Nazifi Ishaq Bichi zuwa ga majalisar dokokin Kano domin tantance shi ya maye gurbin Baba Impossible.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button