Budurwa ta siyar da iPhone guda 20 da ta amsa wurin samarinta ta siya dallelen gida
Mutane sun dinga cece-kuce bayan samun labarin budurwar da ta siyar da wayoyi kirar iPhone guda 20 wadanda ta amsa daga hannun samarinta, Legit.ng ta ruwaito.
An samu bayani kan yadda ta samu ta siya katafaren gida da kudin wayoyin saboda tsabar dabara irin tata. Budurwar ta ce ta roki samari daban-daban wayoyin wadanda babu wanda bai ba ta waya ba a lokacin.
Ya bayyana cewa tana hada wayoyin gabadaya a wurinta, sai ta siya wa kanta gida musamman wanda mutane suka dinga mamaki.
Wani ma’aboci amfani da Twitter, Kalu Ajag ya bayyana nashi tunanin inda yace wannan ne labari mafi ban al’ajabi da ya karanta a 2022. A kalamansa:
“Wannan ne labari mafi rikicewa da na karanta a 2022. Budurwa ‘yar China ta amshi wayoyi kirar IPhone a hannun samarinta guda 20 kuma ta bi ta siyar.”
Legit.ng ta bibiyi labarin inda ta gano cewa tun 2016 jaridar BBC ta wallafa wannan labarin. Yayin tabbatarwa, tabbas lamarin ya faru ne a China, kuma an gano sunan budurwar pseudonym, Xiaoli.
Bisa yadda labarin ya zo, Xiaoli ba diyar masu hannu da shuni bace, kuma ta yiwu ta yi amfani da wannan salon ne wurin siya wa iyayenta gida.
A shekarar 2016 iPhone 7 ce wayar da ake yayi kuma ta kai kimar £14,500, wato kusan Naira miliyan 7.8 a can jin yanzu.
Kamfanin Hui Shou Bao, wanda yake harkar wayoyi ya tabbatar da cewa sun siya wayoyin ne a hannun budurwar.
[Via]