Labarai
An fara yajin aikin sai baba ta gani a Najeriya
A ranar Litinin 28 ga watan Satumba,2020 ne, ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya ke fara yajin aikin sai baba ta gani a fadin ƙasar don nuna rashin amincewarsu da ninka farashin wutar lantarki, da ƙarin farashin man fetur da kuma abin da suka kira tsadar rayuwa.
Kungiyoyin kwadagon sun bayyana cewa ƙarin farashin zai daɗa jefa talakawan Najeriya cikin wahala.
Ana sa ran yajin aikin sai na abin da hali ya yi wanda hadaddiyar kungiyar kwadago ta Najeriya ke jagoranta a fadin kasar zai kassara ayyuka a bangaren gwamnati da ma bangaren masu zaman kansu.
Kungiyoyin kwadagon sun ce ba za a yi ayyuka a ma’aikatun gwamnati da bankuna da kuma filayen jiragen sama ba, haka kuma ana ganin yajin aikin zai shafi asibitoci da sufurin motoci.
Bbchausa ta kara da cewa,Kazalika kungiyoyin kwadago da na farar hula za su gudanar da zanga-zangar lumana a manyen biranen kasar ciki har da Abuja babban birnin tarayyar Najeriyar.
Babbar manufar yajin aikin ita ce domin su karawa matsawa gwanati lamba a kan ta janye matakan da ta dauka a baya-bayannan da suka jibanci tattalin arziki.
Matakan kuwa sun hadar da cire tallafin da gwamnatin ke bayarwa a kan farashin man fetir abin da ya janyo farashin man ya karu da kimanin kashi 11 cikin 100.
Akwai kuma matakin ninka farashin wutar lantarki da aka yi wanda tuni ya fara janyo guna-guni daga ‘yan kasar wadanda ke cewa kamfanonin rarraba wutar lantarkin sun fara tsuga musu kudin wutar da ya wuce tunaninsu.
Tuni dai gwamnatin Najeryar ta ce, ya zama wajibi ta dauki wadannan matakai domin tallafawa tattalin arzikin kasar da kuma tsimin kudaden shiga saboda tattalin arzikin ya gamu da illa sakamakon faduwar farashin danyen man fetir a kasuwar duniya.
Gwamnatin Najeriyar ta ce nan gaba ‘yan kasar zasu ga alfanun daukar wadannan matakai.
To sai dai kuma ana su bangaren kungiyoyin kwadagon
sun ce matakan na gwamnatin shugaba Buhari, zasu kara jefa talakawa ne cikin kuncin rayuwa.
sun ce matakan na gwamnatin shugaba Buhari, zasu kara jefa talakawa ne cikin kuncin rayuwa.
Kungiyoyin kwadagon sun ce yakamata gwamnatin Najeriyar ta fara magance matsalar facaka da cin hanci da rashawa wajen tafiyar da lamuran gwamnati a maimakon kare-karen farashin abubuwan jin dadin rayuwar jama’a.
‘Yan Najeriya dai na kokawa da halin da suke ciki na kunci da tsadar rayuwa, lamarin da wasu daga cikin ‘yan kasar ke goyon bayan yajin aikin.
Ana fara yajin aikin ne bayan da kungiyoyin suka bai wa gwamnati wa’adin makwanni biyu kan ta janye matakan, sannan bangarorin biyu suka kwashe kwanaki suna tattaunawa amma suka kasa cimma
Matsaya.
Madogara : bbchausa.com
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com