Labarai

Ba zan yi hirar kuɗi da wanda bai samu dala miliyan 100 a bana ba — Burna Boy

Ba zan yi hirar kuɗi da wanda bai samu dala miliyan 100 a bana ba -- Burna BoyShahararren mawakin nan da ya lashe kyautar Grammy, Burna Boy, ya bayyana cewa ba zai yi hirar kuɗi da kowa ba idan bai samu dala miliyan 100 a bana ba. Naijaloaded ma ta ruwaito wannan labarin

 

Ya bayyana hakan ne ta InstaStory a shafinsa na Instagram a jiya Lahadi, inda ya ce, “Ba zan iya yin magana ta kuɗi ba idan ba ku samu $100m a wannan shekara ba.”

Hakan na zuwa ne sa’o’i bayan abokin aikinsa, Wizkid ya yi alfahari game da adadin dukiyar da ya tara.

Wizkid har ma ya yi alkawarin buɗe aji ga masu sha’awar su zo su koyi yadda za su sami duk abin da su ke so da kuma iya tattala kuɗi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button